Sunday, 1 April 2012
ABIN DA WANNAN MUDAWWANAR (Blog) TA KUNSA
SALAM , zan dauki yan mintuna nayima bayanin abin da wannan mudawwanar (blog) ta kunsa, zan fara da tarihin kaina an haifeni a unguwar Zango cikin birnin kano Najeriya shekara 21 da suka gabata, yawan neman ilimi ya kai ni karkara kuma yawancin abokai na sun fito daga karkara kuma sun kasance manoma inda makaranta ta hada mu. zama tare dasu a karkara cikin gonaki ya sanya min soyayyar wannan harka, wanda wannan yasa na fara koyar noma dakiwo daga wajensu da kuma hanyoyin bunkasa shi musamman a yankin arewacin najeriya wanda ake mai kallon koma baya. Nayi imani ba wani abu mai dadi kuma tabbatacce ga wannan kasa mai albarka da Allah ya ni'imta mu da ita kamar rungumar wannan harka ta noma da kiwo.ta hanyar noma da kiwo babu wani abu na jin dadin rayuwa da zai gagaremu samu a wannan duniya, domin albarkar noma da kiwo yawa ne da ita. kasancewa ta mutum mai yawan tafiye-tafiye naje garuwa daban-daban na halarci tarurruka masu yawa kan yadda za a bunkasa wannan harkar.na ziyarci manoma da gonaki daban-daban wanda ske noma amfani iri-iri da gidajen gona inda ake kiwon kama daga tsutsaye,dabbobi,kifaye,kwari da sauransu wannaan ilimi da nake dashi naga ya zama wajibi na amayar da shi gareku don amfanin ku da kuma wannan yanki namu.Dalilin haka na yanke hukuncin bude wannan mudawwanar don ta zama wata matattara ta bayanai aka abin dana koya ta hanyar gogayyata da manoma,binciken da nai kan wannan harka da tattaunawar da nai da malaman gona, malaman jami'o'i na tsangayar noma da kiwo da fatan zasu zama masu amfani a gareku. Fatana shine manoma da masu sha'awar shiga wannan harka ta noma da kiwo za su karu da abubuwan da zamu tattauna a wannann mudawwar, zamu zuba ido don ganin tambayoyin ku,karin haske da kuma gyra akan abin da muka yi kuskure. Fadakarwa; wannan mudawwana 9blog0 ba su daga cikin manufofinta sayarwa ko tallata wata hajja ko siyasa. babban kudurin mu shine yada bayanai, ta inda zamu dinga kawo muku labarai da dumi-dumin su da suka shafi noma da kiwo,shawarwari da hanyoyin bunkasa wannan harka ta hanyar samun bashi cikin sauki,taki mai inganci da kuma iri. don wannan yanki ya tsere wa sa'a ta fuskar noma da kiwo a duniya baki daya. In Allah ya kai mu lokaci na gaba zan kawo mukala akan tarihin noma da kiwo. nagode.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment