HAMADA DA TALAUCI
Hakikanin gaskiya shine talauci yana kafada da kafada da gari ko kasa dake tare da annobar hamada domin kuwa bincike ya nuna kashi 90 cikin 100 na mutanen da suke rayuwa a kan tudu (dryland) a kasashe masu tasowa suna rayuwa ne cikin talauci da koma bayan tattalin arziki. Wannan matsala ta samo asali ne saboda lalacewar kasar noma da raguwar yawan abin da ake girba duk shekara.Ga wahalhalu na rayuwa da kuma wuya da suke sha kafin su samu kayan aiki na zamani wanda zai rage yawan ayyuka da kuma rage daukar dogon lokaci. Wannan a bayyane yake ga duk wanda yai kyakykyawan nazari a yankin nan namu na arewacin najeriyya wanda binciken masana ya tabbatar da yana cikin yanki da talauci da rashin aikin yi yai kamari, wannan kuwa ya faru ne saboda tasirin da wannan annoba ta hamada tayi wajen toshe dukkan kafofin bunkasar tattalin arzikin wannan yanki wato noma da kiwo.Hamada a wannan yankin namu tana mamayar kamar yadda masana suka fada tafiyar kilomita 6 a duk shekara, inda take rufe kasa ruf, ta haifar da munanan cututtuka iri-iri, ga dumamar yanayi wanda yake sa mutanwe su dinga shakar iska mai tsanann zafi, ga wata iska mai karfi mai tattare da kura wato (guguwa), hakanan yawancin tafkunan mu da rijiyoyin mu suna ta kafewa wanda wannan babbar barazana ce ga manoma da makiyayan mu. Sannan wannan annoba ta hamada ta janyo duk yawancin hanyoyin mu na karkara duk sun mutu, sun zagwanye ta yadda safarar kayan amfanin gona daga karkara zuwa kasuwanni yake zama matsala wanda wannan yake kawo tashin kayayyakin abinci a mafi yawa daga garuruwan wannan yanki namu. Makiyaya kuwa suna fuskanta rama, rashin lafiya da kuzari kai har ta kai ana samun mutuwar dabbobi saboda karancin wajen kiwo da kuma kafewar kogunan mu inda nan ne mashayar yawancin wadannan dabbobi.
SAKAMAKON HAMADA
Sakamakon wannan annoba ta hamada an samu kaura sosai inda yawancin mutanen karkara suke barin kauyuka suna komo wa birni saboda matsananci halin da suke ciki, wanda wannan ya haifar da rashin aikin yi saboda yawan mutanen da suke kwararowa cikin birni ba kaukautawa, kaza lika yawan harkoki marasa kyawu irn su fashi,damfara da sauransu sai karuwa suke yi. Hakanan can karkara yawanci tana zama kufai ba damar ayi noma saboda yashi ya cinye gonakin mutane wanda wannan ya kawo karanci da tsadar abinci da bamu taba fuskantar saba a tarihin wannan kasa, inda kullum kayan abinci da na masarufi farashin kara sama yake. Matsalar samun iska mara dadi me kura ga kafewar rafuna da kogunan mu wato mashayar dabbobin mu na kiwo. Hada-hadar kasuwanci ma tayi kasa sosai saboda wannan annoba wanda ta shafi kowa da kowa ma'ana har gwamnati da shuwagabannin mu domin kudin shiga wato (revenue) yana raguwa ta fuskar hada-hadar kasuwanci da kuma noma da kiwo.
INA MAFITA
Mafita dai farko kamar yadda na fada a baya cewa ita annobar hamada matsala ce da ta shafi kusan kowa da kowa ma'ana gwamnati,manoma,makiyaya,attajirai,talakawa da daidaikun al'umma ashe in kuwa hakane ya zama wajibi mu tashi tsaye mu yaki wannan annobar kafin ta kai ga kayar da mu. Abin da nake ganin mafi muhimmanci shine doka da oda ma'ana kowannan mu yayi kokari wajen kare dokokin da hukumomin gwamnati suke sanyawa kamar hana sare bishiyoyi da kuma yin noma da kiwo bisa ka'ida. Mafita ta biyu shine tona rijiyoyi da kyakykyawan tsari wajen noman rani. Na san dukkan mu mun san cewar masu sare bishiyoyi suna hakane yawanci don yin amfani da icen wajen yin girke-girke da dafe-dafe to anan gwamnati idan ta saukar da farashi tare da wadata al'umma da man kananzir wannan zai sa yan kasa su koma yin amfani da risho don yin girki. ba man kananzir ba har su gawayin kol, iskar gas da sauransu duk zasu taimaka gaya wajen rage yawan kona itace akai-akai. Dashen bishiyoyi ma yana da alfanu sosai wajen yakar hamada, amma a tabbatar in an dasa a samu masu kula dasu har su kai ga kama kasa. Anan zan dakata sai mun hadu a mako nagaba. NAGODE.
Sunday, 24 June 2012
Thursday, 14 June 2012
MAFITA GAME DA KWARAROWAR HAMADA A YANKIN AREWA (1)
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mako a wannan mudawwana tamu ta noma da kiwo wacce take tattauna al'amuran noma da kiwo musamman a wannan yanki namu na arewacin najeriyya. Wannan makon da yardar mai duka zamu tattauna akan wannan bakuwar matsalar nan da tak ci taki cinyewa wato matsalar kwararowar hamada wanda da muke jin labari daga kasashe masu nisa to yau gata a kofar gidanmu illah iyaka muyi kokari wajen samar da mafita kafin wankin hula ya kai mu dare.
Kwararowar hamada na daya daga cikin manyan matsalolin da mafi yawancin jahohin arewacin wannan kasa suke fama da ita. Jahohin nan sun hada da sokoto,kebbi,zamfara,yobe,jigawa kano,bauchi,katsina inda kuma tafi kamari shine jahar borno(inda ta mamaye ku san gabaki dayan yankin kudu na jahar). Inda ta haifar da koma baya a habbakar noma sakamakon mamayar da tulin rairayi yayi wa filayen noman. Har ta kai ga ministan muhalli na najeriyya yayi hasashen cewa a dukkan matsalolin da wannan kasa take fuskanta a bangaren muhalli ,kwararowar hamada ce babbar kalubale na muhalli a kasar nan, wanda in ba an tashi tsaye anyi maganin taba zai haifar da mummunan karancin abinci sakamakon afkuwar fari da hamadar kan haddasa. Bincike ya tabbatar da cewa karancin ruwan sama da ake samu a duk shekara, afkuwar fari da lalacewar kasar noma ya samo asali ne da wannan matsala ta HAMADA.
MENENE HAMADA ?
Hamada kamar yadda muka sani shine lalacewar kasar tudu (dryland). wanda tana faruwa ne sakamakon abubuwa da dama kamar canjin yanayi daga Allah da kuma ayyuka ko mu'amalolin dan'adam na yau da kullum. Haka nan hukumar abinci da noma ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa kwararowar hamada ita ce babbar matsalar muhalli a duk fadin duniya inda suka fassara kwararowar hamada da kyakykyawra kasa ta koma sahara sakamakon saran bishiyoyi,fari, ko noman gona ba bisa ka'ida ba.
TAKAITACCEN TARIHI
Hamada a duk fadin duniya ta samo asali daga yanayi da yake kai kawo a lokaci mai tsawo daya gabata.cikin yawancin wadannan lokuta hamada tana fadada da kawo tasgaro ga ayyukan yau da kullum na dan'adam. Wadansu girman su ya zarce hankali kamar wannan babbar hamada ta duniya wadda ake kira da SAHARA.Kwararowar hamada ta taka rawar gani a zamantakewar dan'adam, inda ta taimaka gaya a wajen faduwar mafi yawa daga manya-manyan daulolin duniya kamar su daular girka, daular rumawa da sauran su.
INDA HAMADA TA SHAFA
Bincike ya nuna wajen kashi 40-41 cikin dari na duniya tudu ne wanda ya zama matsuguni ga mutane kimanin biliyan biyu, sannan an kintaci cewa kashi 10-20 cikin 100 na tudu a halin yanzu hamada ta cinye wanda ya kai gwargwadon murabba'in kilomita miliyan 6-12, ya nuna kenan kashi 6 cikin 100 a halin yanzu suna rayuwa ne a cikin hamada, sannan akwai kimanin mutane biliyan daya da suke cikin dar-dar na mamayar hamada .kamar yadda muka fada a baya cewa SAHARA ita ce babbar hamada a duk fadin duniya a halin yanzu tana matsawa kudu da gudun kilomita 48 a duk shekara.
ME KE KAWO HAMADA.
Sannan abin da yake kawo wannan annobar ta hamada shine mummunar dabi'ar nan ta nutanen mu na yawan sare bishiyoyi ba bisa ka'ida ba, sannan ko da an sare don wata bukatar zaka ga shi ke nan ba za'a sa wata a madadin wannan wadda aka sare ba. Abi na biyu shine yawan noman gona akai-akai ba kakkautawa, domin yawan noman gona yana sa sinadaran dake cikin kasa su kare dai-dai lokacin da ba zata iya samar da wadan suba. Wannan yafi faruwa ga masu noman rani shine nake ganin ya kamata nai kira ga manoman rani da su tabbata suna bin shawarar kwararru don kaucewa irin wadannan matsaloli. In Allah ya kai mu lokaci na gaba zamu dora a inda muka tsaya. NAGODE

Sunday, 10 June 2012
NOMAN MASARA (2)
Barkan mu da sake saduwa a wannan mako inda muke bayani akan amfanin gona mafi samun daukaka a tsakanin yan'uwansa wato masara, in baku manta ba wancan mako mun yi gabatarwa da takaitaccen bayani da asalin masara da yardar mai duka wannan mako zamu tsunduma yin bayani akan yadda ake noman masara domin kara fadada ilimi da kuma sabbin dabarun shuka na zamani.
Abin na farko wanda na san duk manomin masara ya san wannan shine dole kowace gona da za ai noman masara a cikinta ya kasance a tudu take wato ma'ana bata rike ruwa ko kuma da anyi ruwa nan da nan zata shanye shi a dan lokaci kalilan, sannan ya kasance gonar ta zama tana dauke da albarka wato (nutrient) wanda zasu bawa irin masara taimako wajen saurin fitowa. Kenan mun fahimci cewa noman masara ba a kowace gona ya kamata ayi ba dole sai an bincika an samu wadda ta cika wadannan siffofi da muka ambata a sama.Masana sun raba masarar mu zuwa gida biyu kamar haka ;
(1) MASARAR ZAMANI : wato wadda muke ganin ta da farin jiki ko yalo iri masarar zamani yana da yalwa sosai domin manomi ya kan girbi masara da takai Tan 3 zuwa 7 a duk kadada daya bayan haka kuma yana da surin fitowa. Domin kuwa daga fitowarsa ba zai kwana 100 ba zai kosa ga kuma juriya daga kwari da cututtuka kuma koda a kwari ne akan ioya shuka ta kuma ta fito.
(2)MASARAR GARGAJIYYA: Masarar mu ta dauri tana da iri kala-kala kuma a kan hadata da sauranv amfanin gona kamar wake,gyada da sauransu, sannan tana ba da amfani mai yawa in aka girbe.
lokutan shuka masara a wannan yanki namu kamar yadda muka sani shine wannan yanki namu kamar yadda mu kai bayani a baya cewa damunar mu bata da tsayi shine nake ganin zan bawa manoman mu na masara shawarar cewa daga watan hudu zuwa na biyar su tabbatar sun shuka masarar su domin masarar ta kosa da wuri kamar yadda muka fada a baya. Sannan a kiyayi yin noman masara akasan inda itatuwa suka lullube don a kaucewa lullumi wanda yake zama illa ga girma da kosawar masara.
Masarar mu ta gargajiyya mai kalar ja da fara za'a shuka irin ta mai nauyin kilo 18 a cikin kowace kadada daya. Akan sa daya ko biyu cikin kowane rami. Sannan yana da kyau a bar ratar kamu uku a tsakanin kowace shuka. Yayin da masarar zamani kamar yadda masana suke bayar da shawara cewar ya kamata a dinga barin ratar santimita (centimeter) 90 yayin da tsakanin kunya zuwa kunya a dinga barin santimita 34.Ana bukatar iri mai nauyin Tan 25 a kowace kadada daya inda za'a dinga sa iri biyu a duk rami daya.
Abi na gaba shine taki wanda mukai mukalar sa a baya, to masara akan watsa mata takin zamani ko na gargajiyya. Manomin masara kan iya watsa taki a gonarsa kafin yayi shuka ko kuma bayan yayi shuka, a lura cewa ba kowane taki na zamani ko na gargajiyya ba za'a watsa a gonar masara ba wato ya kasance an tantance wane taki ne zaifi dacewa ga masara.
Masara na bukatar nome ciyayin da suke kusa da ita kafin ta girma, sannan anai mata feshin maganin kwari

Sunday, 3 June 2012
NOMAN MASARA 1
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mudawwana ta noma da kiwo da fatan ana samun waraka daga abubuwan da muke tattaunawa a wannan mudawwana tamu Allah yasa mu dace AMIN.A wannan mako zamu yi bayani ne akan wannan amfanin gonar mai dadadden tarihi, mai gina jiki da kuma juriya daga kwari. Bincike ya tabbatar da ana girbe sama da tan miliyan 800 na wannan amfani gona a fadin duniya. Da yardar maiduka zamu tattauna ne akan Asali, takaitaccen tarihin masara, yadda ake noman masara musamman a wannan yanki namu da kuma alfanun dake tattare da wannan amfani gona mai tsohon zamani.
TAKAITACCEN TARIHI
Masara tana daga dangin ciyayin nan da ake kira da GENIUS POECAE, wanda suka kunshi fiye da kala dubu na na ciyayi. Masara kamar yadda muka sani tana da yanayi da hatsi kamar Alkama, Dawa da sauran su.Hujjojin kimiyyar aikin gona sun tabbatar da cewa yabanyar da a yanzu muka santa da Masara an fara gano tane wajen shekaur 7000 kafin haihuwar Annabi Isa da suka shude, daga cikin ganyayyakin dajin nan wato TOASINTE. Masarar yanzu ta sha ban-ban data waccan zamani domin kuwa kusan har yawancin manoman mu na yanzu bana tsammanin sun san cewa waccan masara ta dauri tafi ta wannan zamani kankanta da dandano ba kamar irin ta yanzu ba. Haka abin yaci gaba da tafiya har zuwa shekara ta 1500 kafin haihuwar Annabi Isa, inda turawan daji (mesoamerican) suka zamanantar da masara tahanyar amfani da dabarun noma zuwa yadda muke ganin ta a yau. A karni na 16 zuwa na 18 ne, noman Masara ya bunkasa ya shiga dukkan sasannin duniya sakamakon mulkin mallakar turawa, wannan yasa sukekai irin Masara nahiyoyi da dama kuma ya samu damar karbuwa ga kusan dukkan mutane.
AMFANIN MASARA
Kadan daga cikin amfani da ake da masara shine ana sarrafata a mai da ita gari don yin Tuwo, Kunu da sauransu, idan an tankade ta tsakin ana baiwa dabbobi a matsayin abinci. Hakanan masana'antun maganin zazzabi ma suna amfani da masara domin hade-haden magungunan su da kuma kamfanonin lemuna da makamantansu.Ba haka nan kadai ba kamfanonuwan tufafi ma suna amfani da masara wani zubin a madadin roba.
ADADIN NOMAN MASARA
Bincike ya tabbatar da Masara ita ce amfanin gonar da aka fi nomawa a duniya, adadin da ake noma wa kamar yadda hukumar noma da abinci ta majalisar dinkin duniya ta wallafa a shekarar 2005 ya nuna ana noman masara da yakai tan miliyan 692 a duniya.Kasar Amurka inda aka fi noman masara suna noma kashi 40 cikin 100 sauran kakashen da suke mara mata baya sun hada da Cana,Meziko,Indunusiya,Indiya,Faransa, da kuma Ajentina. Binciken baya-bayannan ya nuna ana noma tan miliyan 817 na Masara a duniya inda ake noma kadada miliyan 159.In Allah ya kai mu mako na gaba zamu yi bayani yadda ake noman masara musamman a wannan yanki namu. NAGODE.

Subscribe to:
Posts (Atom)