Sunday, 24 June 2012

MAFITA GAME DA KWARAROWAR HAMADA A AREWA (2)

HAMADA DA TALAUCI
Hakikanin gaskiya shine talauci yana kafada da kafada da gari ko kasa dake tare da annobar hamada domin kuwa bincike ya nuna kashi 90 cikin 100 na  mutanen da suke rayuwa a kan tudu (dryland) a kasashe masu tasowa suna rayuwa ne cikin talauci da koma bayan tattalin arziki. Wannan matsala ta samo asali ne saboda lalacewar kasar noma da raguwar yawan abin da ake girba duk shekara.Ga wahalhalu na rayuwa da kuma wuya da suke sha kafin su samu kayan aiki na zamani wanda zai rage yawan ayyuka da kuma rage daukar dogon lokaci. Wannan a bayyane yake ga duk wanda yai kyakykyawan nazari a yankin nan namu na arewacin najeriyya wanda binciken masana ya tabbatar da yana cikin yanki da talauci da rashin aikin yi yai kamari, wannan kuwa ya faru ne saboda tasirin da wannan annoba ta hamada tayi wajen toshe dukkan kafofin bunkasar tattalin arzikin wannan yanki wato noma da kiwo.Hamada a wannan yankin namu tana mamayar kamar yadda masana suka fada tafiyar kilomita 6 a duk shekara, inda take rufe kasa ruf, ta haifar da munanan cututtuka iri-iri, ga dumamar yanayi wanda yake sa mutanwe su dinga shakar iska mai tsanann zafi, ga wata iska mai karfi mai tattare da kura wato (guguwa), hakanan yawancin tafkunan mu da rijiyoyin mu suna ta kafewa wanda wannan babbar barazana ce ga manoma da makiyayan mu. Sannan wannan annoba ta hamada ta janyo duk yawancin hanyoyin mu na karkara duk sun mutu, sun zagwanye ta yadda safarar kayan amfanin gona daga karkara zuwa kasuwanni yake zama matsala wanda wannan yake kawo tashin kayayyakin abinci a mafi yawa daga garuruwan wannan yanki namu. Makiyaya kuwa suna fuskanta rama, rashin lafiya da kuzari kai har ta kai ana samun mutuwar dabbobi saboda karancin wajen kiwo da kuma kafewar kogunan mu inda nan ne mashayar yawancin wadannan dabbobi.
SAKAMAKON HAMADA
Sakamakon wannan annoba ta hamada an samu kaura sosai inda yawancin mutanen karkara suke barin kauyuka suna komo wa birni saboda matsananci halin da suke ciki, wanda wannan ya haifar da rashin aikin yi saboda yawan mutanen da suke kwararowa cikin birni ba kaukautawa, kaza lika yawan harkoki marasa kyawu irn su fashi,damfara da sauransu sai karuwa suke yi. Hakanan  can karkara yawanci tana zama kufai ba damar ayi noma saboda yashi ya cinye gonakin mutane wanda wannan ya kawo karanci da tsadar abinci da bamu taba fuskantar saba a tarihin wannan kasa, inda kullum kayan abinci da na masarufi farashin  kara sama yake. Matsalar samun iska mara dadi me kura ga kafewar rafuna da kogunan mu wato mashayar dabbobin mu na kiwo. Hada-hadar kasuwanci ma tayi kasa sosai saboda wannan annoba wanda ta shafi kowa da kowa ma'ana har gwamnati da shuwagabannin mu  domin kudin shiga wato (revenue) yana raguwa ta fuskar hada-hadar kasuwanci da kuma noma da kiwo.
INA MAFITA
Mafita dai farko kamar yadda na fada a baya cewa ita annobar hamada matsala ce da ta shafi kusan kowa da kowa ma'ana gwamnati,manoma,makiyaya,attajirai,talakawa da daidaikun al'umma ashe in kuwa hakane ya zama wajibi mu tashi tsaye mu yaki wannan annobar kafin ta kai ga kayar da mu. Abin da nake ganin mafi muhimmanci shine doka da oda ma'ana kowannan mu yayi kokari wajen kare dokokin da hukumomin gwamnati suke sanyawa kamar hana sare bishiyoyi da kuma yin noma da kiwo bisa ka'ida. Mafita ta biyu shine tona rijiyoyi da kyakykyawan tsari wajen noman rani. Na san dukkan mu mun san cewar masu sare bishiyoyi suna hakane yawanci don yin amfani da icen wajen yin girke-girke da dafe-dafe to anan gwamnati idan ta saukar da farashi tare da wadata al'umma da man kananzir wannan zai sa yan kasa su koma yin amfani da risho don yin girki. ba man kananzir ba har su gawayin kol, iskar gas da sauransu duk zasu taimaka gaya wajen rage yawan kona itace akai-akai. Dashen bishiyoyi ma yana da alfanu sosai wajen yakar hamada, amma a tabbatar in an dasa a samu masu kula dasu har su kai ga kama kasa. Anan zan dakata sai mun hadu a mako nagaba. NAGODE.

No comments:

Post a Comment