Monday, 25 November 2013

TURAKU GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (2)

                                                         TURAKU GOMA SHA DAYA NA
                                                            CIN NASARA A HARKAR
                                                                NOMA DA KIWO (2)



(6) Yaya kana da dagiya kan al'amura? gudanar da harkar noma na da wahalar gaske, wanda wannan zai iya janyo wa mutum gazawa a wadansu lokutan. Saboda yawancin  mamallakan wannan harka sukan gaza wajen daukar nasara ko rashinta.  Don haka kana bukatar ka dunga samun karfafa gwuiwa a kowanne lokaci don cigaba da dorewar  wannan harka, da kuma kariya daga gurguncewar harkar da makamantansu. Domin kuwa da wannan harka tana da sauki gaya da kaga kowa   a cikin ta.  Anan ya kamata mu ari karin maganar nan da take cewa  idan kana son kayi sukuwar sallah a wannan harka ta noma da kiwo, dole ka zamto ka shirya faduwa daga kan dokin ka sau shurin masaki ba tare daka sare ba.


(7) Yaya harkar noma zai shafi iyalanka? Babu tantama cewar a farkon lokacin daka fara wannan harka  zai dan shafe ka da yarda kake gudanar da harkokin iyalanka ta bangaren  kudi.  Wannan kuwa  kan iya daukar watanni kai har shekaru ma kafin akai ga fara cin riba. Don haka wajibi ka shirya yadda zaka dan gyatta yadda kake gudanar da wadannan harkoki damin samun alheri mai yawa nan gaba kadan.


(8) Shin ka dau wadataccen lokaci kana nazari kan wannan harka don ganin ko akwai alheri a ciki kuwa? Kai sani zaka shiga harkar noma da kiwo ne da nufin samun alheri. Don haka kada kai gaggawa ba  tare daka shirya fuskantar kalubalen dake tattare  da wannan harka ba. Yana da kyau ka halarci tarurruka na karawa juna sani, sayen littafai na harkokin noma da kiwa da jaridu, mujallu da kuma mudawwanoni na wannan harka kamar dandalinnomadakiwo.blogspot.com.


(9) Shin kana da gogewa  kan irin harkar da zaka gudanar?  Yawancin wadanda suka cigaba sukai kaurin suna a wannan harka sun kasance suna da gogewa a wannan harka tun kafin sukai ga shiga cikinta ka'in da na'in. Ka halarci lakcoci kan wannan harka tun kan ka kai da fara wannan harka.


(10) Shin kana da karfin jari?  Rashin kudi   yawanci shine kashin bayan karya ko  gurgunta yawancin harkokin kasuwanci bawai kawai noma da  kiwo ba. Don haka kana  bukatar jari wadatacce domin gudanar da wannan harka yadda ya kamata.



(11) Shin kana iya sayarwa?  Kowanne  iri harkar kasuwanci na bukatar abokan hulda wato (customers) , wanda ake bukatar ka ka fara tuntuba tun farkon lokacin fara gudanar da wannan harka.  Yana da kyau kayi kokari kan bunkasa bangaren daya shafi saye da kasuwanci na wannan harka domin kuwa in dai hajarka bata karbu ba to kuwa wannan ya zama abin da ake kira anyi ba ai ba.



Da wadannan muhimman tambayoyi guda goma sha daya muke ganin duk wanda ya samu damar amsasu yadda ya kamata, zai shiga wannan  harka ta fatan samun nasara gwaggwaba na bada dadewa ba. Allah ya sanya albarka ya taimake mu akan dukkanin al'amuran mu na alkhairi kuma ya datar damu akan yin daidai. Da yardar mai-duka mako mai zuwa zamu tattauna abin da ya shafi kiwo.  NAGODE


Monday, 18 November 2013

TURAKUN GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (1)

                                          TARAKU GOMA SHA DAYA NA CIN
                                               NASARA A HARKAR NOMA
                                                        DA  KIWO (1)


Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mako a wannan dandali namu  mai albarka na dandalin noma da kiwo inda mukan tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo tare da yin tsokaci kan wadansu muhimman bayanai na masana da nufin yin wukar gindi dasu domin fadakar da al'umarmu na birni da karkara kan yadda zamu cicciba wannan muhimmiyyar sana'a tamu ta noma da kiwo da muka gada tun iyaye da kakanni. Allah kadai muke roko ya karba mana kuma ya inganta mana kasar nomanmu da kiwo domin cigaban tattalin arzikin wannan kasa tamu  mai tarin albarka. A yau da yardar mai-duka zamu tattauna ne akan wadansu turaku ko dabaru muhimmai kan yadda masu wannan harka ta noma  da kiwo zasu kai ga bunkasa sana'arsu.

A kasance tare damu.



GABATARWA.



Yana da  kyau ga duk mai  niyyar shiga wannan harka ta noma da kiwo ya kwan da sanin cewa akwai hadurra dake cikin wannan harka wanda hakan ke nuna cewa samun nasara a cikin ya ta'allaka kacokan ga sa'a da kuma bin abubuwa sau da kafa.  Samun  nasara a wannan harka ta noma da kiwo ya dogara da irin hangen nesa da kuma kyakkyawan tsari wajen gudanar da wannan harka mai tsananin riba.  Fara wannan harka ta noma da kiwo zai bawa  mutum damar  da yake bukata ta zama mai dogaro da kansa, amma kafin ka kai ga farawa  ya kamata ka fara bincikar kanka  ta hanyar da zaka gane inda kake da karfi da kuma inda kake da rauni wajen gudanar da wannan harka ta noma da kiwo. Ayin hakan yana da kyau ka tambayi kanka  wadannan muhimman tambayoyi wanda bada amsarsu zai taimaka maka gaya wajen shiga wannan harka ko dakatar da shiga zuwa wani lokaci nan gaba.


(1) Shin kai farin shiga ne?


Kasancewar ka sabo a wannan harka yana da kyau ka zama ka samu dukkan karfi da zuciya da zaka iya jurewa wannan aiki, da kuma daukar muhimman tsarirrika da zasu taimakawa  cigaban wannan harka ta noma da kiwo.  Harkar noma da kiwo na bukatar kwazo da aiki tukuru, yana bukatar kokari da juriya da zai baka damar yin aiki mai yawa a kowacce rana wanda ba zasu yiwu ba har sai ka tursasawa kanka yinsu.


(2) Yaya mu'amalarka take da sauran mutane?

A matsayinka na manomi nasararka tana da alaka da yadda dangantakar ka ta kasance da sauran mutane, wadanda suka hada da sauran yan'uwa manoma, abokan ciniki, cibiyoyin bincike kan harkar data shafi noma da kiwo,dillalai,bankuna, lawyoyi, masana harkar shige da ficen kudi, mutanen garinku, da kuma sauran al'umma. Yana da kyau ka tabbatar ka fitar da nagartattun hanyoyi da zasu taimaka wajen biyan bukatun abokan cinikinka.


(3) Shin ka iya daukar matakai masu kyau?

Ana gane shugaba ne ta hanyar daukar matakai masu kyau, don haka ana bukatar manoma su dunga daukar matakai akan lokaci, cikin gaggawa, domin tabbatar da samun nasara a wannan harka ta noma da kiwo.


(4) Shin kana da karfi na zahiri da karfin zuciya na iya gudanar da wannan harka?


Gudanar da harkar noma da kiwo na bukatar mai da hankali kacokan ga mai gudanar da wannan harka. Babu batun buya ko labewa ga mai yin wannan harka a matsayin ta na yar lelenka. Ko uwa tana guduwa wajen shayar da yarta ne? Kasancewar ka a wannan harka yana da dadi duk da cewa akwai ayyuka masu yawa da kalubalai. Dole ka tsara lokutan ayyukan ka , amma a lura duk abin daya kamata ayi a tabbatar anyi shi akan lokaci cikin gaggawa.


(5) Shin kana da tsari mai kyau da iya gudanarwa?


Kamar yadda muka sani cewar rashin tsari shine babban abin da yake rugurguza yawancin harkoki ba ma kawai na noma da kiwo ba. Kai sani cewa tsarin gudanar da harka mai kyau yana taimakawa wajen kaucewa hadurra masu yawa.


Anan zamu dakata da yardar Allah zamu dora a mako na gaba.  NAGODE.

Monday, 4 November 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (6)

NOMAN WAKEN-SUYA  (6)



Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da  suka  shafi noma da kiwo wani zubin kuma muyi tsokaci kan wani cigaba ko wata ribar kafa da aka samu duka fatanmu shine bunkasa tattalin arzikin wannan kasa tamu wadda Allah madaukakin sarki ya albarkaceta  da  dukkan abin da dan adam ke bukata a rayuwarsa. Idan mai karatu bai manta a makon daya gabata  a cikin wannan mukala tamu mai albarka ta noman waken-suya muna tattauna abin daya shafi yadda za'a magance ciyayi da ka iya addabar  waken-suya  a cikin gona. Da yardar mai-duka a wannan mako zamu kammala wannan mukala. Ku biyo mu.


KWARIRRIKA DA YADDA ZA'A MAGANCESU A GONA YAYIN NOMAN WAKEN-SUYA.

Akwai kwarirrika nau'i daban-daban a cikin gona yayin da ake noman waken-suya, amma binciken masana ya tabbatar da cewa kadan ne cikin wadannan kwarukan masu amfani   ga waken-suya. Kuma masanan sun tabbatar da cewa jinsunan kwarirrika masu cutar da waken-suya a wannan kasa kadan ne,wanda ba zai bada wata babbar wahala ba wajen magancesu.  Babbar hanyar magance barnar kwari  a cikin gonar waken-suya shine ta hanyar amfani damaganin feshin kwarin  nan na CYPERMETHRIN+DIMETHOATE da ya kai alkaluma 100 na ma'aunin (ML) a cikin adadin litar ruwa 15.


CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA YADDA ZA'A MAGANCE SU.

Cututtukan dake addabar waken-suya a wannan kasa su kan yi tasiri sosai wajen hana shi yin yado. Hanyoyin da manomi zai bi kuwa domin magancesu sun hadar  da;

-shuka irin waken-suya mai juriya: wannan itace dabara mafi dacewa awajen maganin cututtukan dake addabar waken-suya.

-Yin gyara da sharar gona mai kyawu: kuma manomi ya kiyayi shuka waken-suya akan busasshiyar kasa.

-Shuka irin da aka tufatar dashi da maganin kasahe kwari da cututtuka: kamar yadda mukai bayani a baya.

-Noman hadaka da sauyi wajen noma waken suya da masara: yin hakan na karawa gona tagomashin daya kamata wajen yaki da cututtuka.

-Ta hanyar  yin amfani  da magungunan  yaki da  cututtukan dake  addabar waken-suya a cikin gona.



             GIRBE WAKEN-SUYA


Yawanci kamar yadda muka sani waken suya na isa girbi yayin da yakai wata 3 zuwa 4 da shukawa. Bayan  haka waken-suya  na bukatar gaggawa ta musamman wajen girbi, domin kuwa  kin yin hakan zai iya kawo asara mai  yawa.  Saboda  haka ana so a girbe  waken-suya da anga  kaso 85 cikin 100 ya  koma kalar ruwan kasa. Akan iya girbe waken-suya ta hanyar amfani da  adda,fartanya ko kuma lauje.  Manomi ya  tabbatar ya yanko shukar waken-suya tun daga tushiya.  Daga nan ana bukatar manomi ya shanya waken-suya daya  girbe akan tamfol har zuwa tsawon akalla makonni biyu. Yana da kyau manomi ya guji  yin amfani da hannu wajen girbe waken-suya, domin yin hakan zai iya fitar da sinadaran da waken-suya ya zuba a cikin gona.  Daga bayan manomi ya tabbatar da cewar waken-suyan sa ya bushe yadda ya kamata sai BUGU.  Bugu shine kamar yadda muka sani zuba waken-suya dake cikin konsonsa a cikin buhu sai a dinga duka da icce.


             AJIYAR WAKEN-SUYA


Waken-suya ya bushe yadda ya kamata idan aka kasa gatsa shi  da hakoro ko kuma da dan-yatsu. A zuba kilo 50 ko kuma kilo 100 na waken-suya a cikin buhu mai kyau a rufe a cikin rufaffen rumbu ko kuma kasan inuwa. Manomi ya lura cewa  yiwa waken-suya kyakkyawar  ajiya zai  taimaka masa gaya wajen samun kariya daga kowanne irin lahani ko tawaya da kuma yin  saurin tsiro  yayin da akai niyyar yin  amfani dashi  a matsayin iri a cikin gona.


          KAMMALAWA


A karshe muna sanar da masu karatun mu cewa wannan mukala kan yadda za'a shuka waken suya ta tsaya daga nan, muna  bukatar  ra'ayoyinku akan abubuwan da muka tattauna, kuma in Allah ya bamu yawan  rai zamu tattauna yadda ake sarrafa da kasuwancin waken-suya. NAGODE.