NOMAN WAKEN-SUYA (6)
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo wani zubin kuma muyi tsokaci kan wani cigaba ko wata ribar kafa da aka samu duka fatanmu shine bunkasa tattalin arzikin wannan kasa tamu wadda Allah madaukakin sarki ya albarkaceta da dukkan abin da dan adam ke bukata a rayuwarsa. Idan mai karatu bai manta a makon daya gabata a cikin wannan mukala tamu mai albarka ta noman waken-suya muna tattauna abin daya shafi yadda za'a magance ciyayi da ka iya addabar waken-suya a cikin gona. Da yardar mai-duka a wannan mako zamu kammala wannan mukala. Ku biyo mu.
KWARIRRIKA DA YADDA ZA'A MAGANCESU A GONA YAYIN NOMAN WAKEN-SUYA.
Akwai kwarirrika nau'i daban-daban a cikin gona yayin da ake noman waken-suya, amma binciken masana ya tabbatar da cewa kadan ne cikin wadannan kwarukan masu amfani ga waken-suya. Kuma masanan sun tabbatar da cewa jinsunan kwarirrika masu cutar da waken-suya a wannan kasa kadan ne,wanda ba zai bada wata babbar wahala ba wajen magancesu. Babbar hanyar magance barnar kwari a cikin gonar waken-suya shine ta hanyar amfani damaganin feshin kwarin nan na CYPERMETHRIN+DIMETHOATE da ya kai alkaluma 100 na ma'aunin (ML) a cikin adadin litar ruwa 15.
CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA YADDA ZA'A MAGANCE SU.
Cututtukan dake addabar waken-suya a wannan kasa su kan yi tasiri sosai wajen hana shi yin yado. Hanyoyin da manomi zai bi kuwa domin magancesu sun hadar da;
-shuka irin waken-suya mai juriya: wannan itace dabara mafi dacewa awajen maganin cututtukan dake addabar waken-suya.
-Yin gyara da sharar gona mai kyawu: kuma manomi ya kiyayi shuka waken-suya akan busasshiyar kasa.
-Shuka irin da aka tufatar dashi da maganin kasahe kwari da cututtuka: kamar yadda mukai bayani a baya.
-Noman hadaka da sauyi wajen noma waken suya da masara: yin hakan na karawa gona tagomashin daya kamata wajen yaki da cututtuka.
-Ta hanyar yin amfani da magungunan yaki da cututtukan dake addabar waken-suya a cikin gona.
GIRBE WAKEN-SUYA
Yawanci kamar yadda muka sani waken suya na isa girbi yayin da yakai wata 3 zuwa 4 da shukawa. Bayan haka waken-suya na bukatar gaggawa ta musamman wajen girbi, domin kuwa kin yin hakan zai iya kawo asara mai yawa. Saboda haka ana so a girbe waken-suya da anga kaso 85 cikin 100 ya koma kalar ruwan kasa. Akan iya girbe waken-suya ta hanyar amfani da adda,fartanya ko kuma lauje. Manomi ya tabbatar ya yanko shukar waken-suya tun daga tushiya. Daga nan ana bukatar manomi ya shanya waken-suya daya girbe akan tamfol har zuwa tsawon akalla makonni biyu. Yana da kyau manomi ya guji yin amfani da hannu wajen girbe waken-suya, domin yin hakan zai iya fitar da sinadaran da waken-suya ya zuba a cikin gona. Daga bayan manomi ya tabbatar da cewar waken-suyan sa ya bushe yadda ya kamata sai BUGU. Bugu shine kamar yadda muka sani zuba waken-suya dake cikin konsonsa a cikin buhu sai a dinga duka da icce.
AJIYAR WAKEN-SUYA
Waken-suya ya bushe yadda ya kamata idan aka kasa gatsa shi da hakoro ko kuma da dan-yatsu. A zuba kilo 50 ko kuma kilo 100 na waken-suya a cikin buhu mai kyau a rufe a cikin rufaffen rumbu ko kuma kasan inuwa. Manomi ya lura cewa yiwa waken-suya kyakkyawar ajiya zai taimaka masa gaya wajen samun kariya daga kowanne irin lahani ko tawaya da kuma yin saurin tsiro yayin da akai niyyar yin amfani dashi a matsayin iri a cikin gona.
KAMMALAWA
A karshe muna sanar da masu karatun mu cewa wannan mukala kan yadda za'a shuka waken suya ta tsaya daga nan, muna bukatar ra'ayoyinku akan abubuwan da muka tattauna, kuma in Allah ya bamu yawan rai zamu tattauna yadda ake sarrafa da kasuwancin waken-suya. NAGODE.
No comments:
Post a Comment