Monday, 18 November 2013

TURAKUN GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (1)

                                          TARAKU GOMA SHA DAYA NA CIN
                                               NASARA A HARKAR NOMA
                                                        DA  KIWO (1)


Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mako a wannan dandali namu  mai albarka na dandalin noma da kiwo inda mukan tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo tare da yin tsokaci kan wadansu muhimman bayanai na masana da nufin yin wukar gindi dasu domin fadakar da al'umarmu na birni da karkara kan yadda zamu cicciba wannan muhimmiyyar sana'a tamu ta noma da kiwo da muka gada tun iyaye da kakanni. Allah kadai muke roko ya karba mana kuma ya inganta mana kasar nomanmu da kiwo domin cigaban tattalin arzikin wannan kasa tamu  mai tarin albarka. A yau da yardar mai-duka zamu tattauna ne akan wadansu turaku ko dabaru muhimmai kan yadda masu wannan harka ta noma  da kiwo zasu kai ga bunkasa sana'arsu.

A kasance tare damu.



GABATARWA.



Yana da  kyau ga duk mai  niyyar shiga wannan harka ta noma da kiwo ya kwan da sanin cewa akwai hadurra dake cikin wannan harka wanda hakan ke nuna cewa samun nasara a cikin ya ta'allaka kacokan ga sa'a da kuma bin abubuwa sau da kafa.  Samun  nasara a wannan harka ta noma da kiwo ya dogara da irin hangen nesa da kuma kyakkyawan tsari wajen gudanar da wannan harka mai tsananin riba.  Fara wannan harka ta noma da kiwo zai bawa  mutum damar  da yake bukata ta zama mai dogaro da kansa, amma kafin ka kai ga farawa  ya kamata ka fara bincikar kanka  ta hanyar da zaka gane inda kake da karfi da kuma inda kake da rauni wajen gudanar da wannan harka ta noma da kiwo. Ayin hakan yana da kyau ka tambayi kanka  wadannan muhimman tambayoyi wanda bada amsarsu zai taimaka maka gaya wajen shiga wannan harka ko dakatar da shiga zuwa wani lokaci nan gaba.


(1) Shin kai farin shiga ne?


Kasancewar ka sabo a wannan harka yana da kyau ka zama ka samu dukkan karfi da zuciya da zaka iya jurewa wannan aiki, da kuma daukar muhimman tsarirrika da zasu taimakawa  cigaban wannan harka ta noma da kiwo.  Harkar noma da kiwo na bukatar kwazo da aiki tukuru, yana bukatar kokari da juriya da zai baka damar yin aiki mai yawa a kowacce rana wanda ba zasu yiwu ba har sai ka tursasawa kanka yinsu.


(2) Yaya mu'amalarka take da sauran mutane?

A matsayinka na manomi nasararka tana da alaka da yadda dangantakar ka ta kasance da sauran mutane, wadanda suka hada da sauran yan'uwa manoma, abokan ciniki, cibiyoyin bincike kan harkar data shafi noma da kiwo,dillalai,bankuna, lawyoyi, masana harkar shige da ficen kudi, mutanen garinku, da kuma sauran al'umma. Yana da kyau ka tabbatar ka fitar da nagartattun hanyoyi da zasu taimaka wajen biyan bukatun abokan cinikinka.


(3) Shin ka iya daukar matakai masu kyau?

Ana gane shugaba ne ta hanyar daukar matakai masu kyau, don haka ana bukatar manoma su dunga daukar matakai akan lokaci, cikin gaggawa, domin tabbatar da samun nasara a wannan harka ta noma da kiwo.


(4) Shin kana da karfi na zahiri da karfin zuciya na iya gudanar da wannan harka?


Gudanar da harkar noma da kiwo na bukatar mai da hankali kacokan ga mai gudanar da wannan harka. Babu batun buya ko labewa ga mai yin wannan harka a matsayin ta na yar lelenka. Ko uwa tana guduwa wajen shayar da yarta ne? Kasancewar ka a wannan harka yana da dadi duk da cewa akwai ayyuka masu yawa da kalubalai. Dole ka tsara lokutan ayyukan ka , amma a lura duk abin daya kamata ayi a tabbatar anyi shi akan lokaci cikin gaggawa.


(5) Shin kana da tsari mai kyau da iya gudanarwa?


Kamar yadda muka sani cewar rashin tsari shine babban abin da yake rugurguza yawancin harkoki ba ma kawai na noma da kiwo ba. Kai sani cewa tsarin gudanar da harka mai kyau yana taimakawa wajen kaucewa hadurra masu yawa.


Anan zamu dakata da yardar Allah zamu dora a mako na gaba.  NAGODE.

No comments:

Post a Comment