Monday, 30 September 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (1)

                                            NOMAN WAKEN SUYA




Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu na noma da kiwo inda muke tattaunawa akan  al'amuran da suka shafi noma da kiwo don bunkasa tattalin arzikin al'umarmu,yankinmu da kuma kasarmu baki daya. A wannan makon da yardar mai-duka zamu tattauna akan noman waken suya. Da fatan masu karatu za'a kasance damu.



GABATARWA

Waken suya na daya daga cikin amfanin gona da aka sansu tun da dadewa a can nahiyar ASHIYA (Asia), wanda suke noman sa dan samar da mai,madara da kuma sauran sinadaran kara kuzari irin su PROTEIN da sauran su. Ana noman waken suya ne a waje mai yanayin zafi. Ainihin manoman waken suya kamar yadda binciken masana ya nuna suna noman shine don samar da takin gargajiyya sakamakon yawan sinadarin nan na NITROGEN da yake kunshe dashi. Musamman ga manoma masu yin noman kewaye wato (crop rotation) inda ake shuka shi a matacciyar gona bayan ya  fito sai su bi shi da kasa su binne daga baya kuma sai a shuka amfani.

Cigaban da aka samu na fasahar zamani ta hanyar sarrafa da adana man waken suya yasa aka samar da hanyoyin amfani dashi daban-daban, wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna akan abin da ya shafi tarihi,asali da cigaban da aka samu a duniya wajen noman waken-suya,wannan ya kunshi  nomansa,cututtuka da kwarikan dake addabarsa da yadda za'a magancesu,yadda ake zuba taki da girbinsa da yadda manomi zai adana shi, da kuma uwa-uba yin tsokaci kan irin muhimmiyar gudummawar da waken-suya ke bayarwa wajen cicciba tattalin arzikin duniya.


TAKAITACCEN TARIHI


Kamar yadda muka fada, yankin Ashiya (Asia) shine yanki na farko kamar yadda masana suka fada da aka fara noman waken-suya,wanda suke noman sa a matsayin dangin furannin dajin nan  da ake kira da (Glycine soja) kusan shekaru 5000 da suka gabata. Duk da haka, asali da tarihin noman waken-suya ba zai cika ba tare da ambaton wannan shararren jarumin nan na kasar Sin (China) wato SHENNONG wanda akewa lakabi da ''DIVINE FARMER'', masana tarihi sun tabbatar da cewa oshine wanda ya kawo fasahar noma ga mutanen kasar Sin da kuma Biyatnam (Vietnam), ance ya sanya wken-suya a cikin furannin daya kira ''Tsarkakakkun furanni guda biyar'' wanda suka kunshi shinkafa,alkama,dawa da kuma gero. Hakanan a shekara ta 1000 kafin haihuwar Annabi Isa aka fara noman waken-suya a kasar Jafan (Japan) da Koriya (Korea) wato tun  a zamanin mulkin Rumawa.
Waken-suya yana daga cikin dangin Legum wanda ya hada da wake da sauran su. Wannan dangi shine na uku mafi girma a dangin furannin kallo, dake dauke da dangi kala-kala har kusan 15,000. Waken-suya a kewaye yake yana dauke da launin ruwan dorawa-dorawa. Saboda yawan maikon da yake dashi da kuma sinadarin PROTEIN daya kunsa yasa akan iya sarrafa waken-suya ta hanyoyi daban-daban domin amfani iri-iri.

Masana tarihi sun tabbatar da cewa noman waken-suya ya bulla a nahiyar turai da kasar Amurka tun a lokacin mulkin mallaka. Hakanan manoman yankin Ashiya sun fara noman waken-suya ne ka'in da na'in a shekarar 1910. Tun daga sannan noman waken-suya ya habbaka a wannan yanki, inda a halin yanzu kasar Amurka ke jagoranta da kashi 55 cikin dari wato (55%) yayin da idan muka dawo yankin mu na Afirika kuma kasarmu ce ta Najeriyya ke jagoranta yayin da kasar Afirika ta kudu (South-africa) ke rufa mata baya.

Da yardar mai-duka zamu dora a mako na gaba. NAGODE

Monday, 23 September 2013

                                                    NOMAN AUDUGA 2


NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA

Masu karatu da fatan kuna tare da mu kuma kun ji dadin mukalar mu ta makon da ya gabata , a yau da yardar mai duka muna dauke da karashen wannan mukala da muke tattaunawa akan noman auduga.


Noman auduga a Najeriyya musamman ma a wannan yankin namu yafi karkata da yin amfani da katti yayin da a sauran sassan duniya ake amfani da taraktocin noma da injina da saukaka wa da kuma saman amfani mai yawa. Auduga na tsananin bukatar ruwa tare da magungunan kashe kwari (wanda binciken masana ya tabbatar da akwai jinsinan kwari sama da 1300, ciki wanda 500 suna wannan nahiyar tamu ta Afirika da suka dogara da auduga dan samun abinci) da kuma wadataccen taki. Bisa ga haka ne ma kasashen Amurka da Hindu wato (India) suka samar da wanisabon irin auduga wanda suka sauya fasalinsa ta hanyar binciken kimiyya wanda suke kira da (Genetics) ko (Genetically modified cotton) ko (GM) a takaice. GM cotton na da tsananin juriya daga kwari da rashin ruwa da kuma sauran cututtuka. Dadin dadawa kuma kwari basa iya cin sa saboda dafin dake tare da shi.
Auduga na bukatar lokacin noma mai tsayi, kasa mai yawa, da haske ga kuma uwa-uba ruwa wanda ake bukatar akalla zira'i biyu, binciken masana harkar noma suntabbatar da saboda bukatar ruwa da auduga ke bukata ya zama silar kwararowar hamada a yankunan tsohuwar tarayyar sobiyat wato (U.S.S.R). A halin yanzu kasar Amurka da sauran kasashen nahiyar Afirika ke jagorantar noman auduga a fadin duniya.


Najeriyya ma ba'a barta a baya ba wajen noman auduga, a matsayinta na daya daga cikin ginshikan ci gaban tattalin arzikin wannan kasa da kuma samar da kudaden shiga tun daga hshekarar 1903 zuwa yau. A kokarin gwamnati na ganin ta bunkasa wannan harka ta noman auduga yasa ta kafa hukumomi da kwamitoci daban-daban don bada shawara kan yadda za'a bunkasa wannan harka. Wadannan hukumomi da kwamitoci siun  hada da British Cotton Growers Association, har ya zuwa shekarar 1974 inda aka maye gurbin ta da Cotton Marketing Board. A sabili da tsarurrukan gwamnati na sauya fasalin tattalin arzikin wannan kasa yasa gwamnati ta rushe wannan hukuma tare da dakatar da ayyukanta tare da kafa wani kwamitin tuntuba a madadinta wanda ta kira da Cotton Consultative Commitee (CCC). Wannan bai tsaya anan ba a shekara 2005 an sake kafa  wani kwamiti mai suna Cotton Development Commitee wanda aka dora alhakin farfado da noman auduga ta hanyar amfani da fasahar zamani don cigaban kasa.


NAHIYOYIN NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA
Duk shekara a noma auduga a abin da ya aki kadada sama da miliyan 0.2-0.6 inda tsaunukan Savannah ke jagorantar kaso mafi yawa. A shekarar 2007-2008 kawai an noma akalla tan 400,000 na irin  auduga a kadada miliyan 0.3. Noman auduga a Najeriyya ya kasu izuwa manyan shiyoyi guda uku sune: shiyyar arewa ke da kashi sittin cikin dari (60%), shiyyar gabas nada kashi talatin cikin dari (30%), yayin da shiyyar kudu keda ragowar kashi goma cikin dari (10%). Kananan manoma masu gona mai girman kadada 3-5 ne suka mamaye noman auduga a najeriyya.




KAMMALAWA 
A karshen wannan mukala ba zamu gajiya kan kira ga mutane da gwamnati kan wajibcin mu na koma da rungumar harkar noma ka'in da na'in domin cicciba tattalin arzikin kasarmu. Gwamnati na da kyakykyarawar da zata taka wajen bunkasa noman auduga ta hanyar tallafawa manoman auduga da kuma karfafawa masu zuba jari kan masana'antun samar da tufa a Najeriyya wadda ita ce masa'anta ta uku wajen tallafawa tattalion arzikin wannan kasa in ka cire danyan man fetur (crude oil) da noma sai masana'antun tufafi wato (textile industries) wanda suka dogara kacokan kan auduga dan yin ayyukan su. Sai mun hadu a mako na gaba. NAGODE

Monday, 16 September 2013

NOMAN AUDUGA 1

                                                  NOMAN   AUDUGA

 Masu karatu inai muku sallama tare da fatan alkhairi da kuma jinjina dan gane da jumurin karatu da kuma fatan alherin da kuke mana tare da kuma neman afuwar ku dangane da shirun da aka ji na yan kwanaki, wannan kuwa ya faru ne saboda tutsun na'ura da muka fuskanta, da fatan za'ai mana afuwa kuma a cigaba da kasancewa damu.A yau zamu tattauna kan abin da ya shafi noma da kasuwancin auduga a kasarnan.

Auduga na daya daga cikin kayan amfani gona da ake sarrafa su dan amfani iri daban-daban, wanda ya hada da sarrafa auduga don samar da tufafin sawa,samar da takardu,samar da magani,samar da mai da sauran kayan abinci. Auduga ana noman ta a ko'ina cikin fadin duniyar nan tamu, yayin da musayar kasuwancinta a kasuwar duniya ya kai sama da Dala biliyan 12 a duk shekara inda kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirika ke jagoranta da kaso mafi rinjaye. Wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna takaitaccen tarihin auduga,ire-iren ta,kasuwancinta,noman ta a yau da kuma bayanin yadda ake sarrafata don amfanin mu na yau da kullum.

TAKAITACCEN TARIHI
Auduga ko Al-qutn da yaren Larabci (Arabic), na daya ga cikin dangin furannin fulawoyin kallo wato (flowering plant). Akwai sanannun ire-iren auduga guda hudu. Akwai wadda ake kira da GOSSYPIUM HIPSUTUM wadda aka fi noman ta a kasashen Amurka,Mexico da kasashen karebiyan (carrebian).Sauran sun hada da TREE-COTTON wadda aka fi noman ta a kasashen Hindu (India) da Pakistan, sai BARBADEBSE ta kasashen kudancin Amurka da kuma LEVANTINE wadda ake noman ta a kasashen Afirika da kuma kasashen gabas ta tsakiya wato (Middle -east).

Masana tarihi sun tabbatar da an fara noman auduga kusan shekaru 6000 da suka gabata, a daular Harrafawa (Harapan) da ke yankin Asiya (Asia), daga nan noman auduga ya bazu,ya yadu zuwa fadin duniya inda Manoma suka dukufa ka'in da na'in wajen nomanta gwargwadon irin yanayin da Ubangiji ya hore musu.

AMFANIN AUDUGA
Auduga na da matukar amfani ga dan-adam ta yadda masana suka tabbatar da cewa matukar mutane zasu rayu to tilas suyi noman auduga. Domin kuwa baya ga amfani da auduga da ake yi don saka sutturun sawa, hakanan ana amfani da ita danyin zaren lilo,ragar kamun kifi,likkafani da sauransu. Saboda yawan alfanu da juriya da biyan bukata na auduga yasa masana'antun tufafi suka dogara kacokan kan auduga don biyan bukatun su.

Kazalika ana amfani da auduga dan magani,abinci da kuma samar da takardu. Kwallon auduga ana amfani dashi wajen dafa abinci sannan kuma naman ta akan ba dabbobi su ci.

Idan maiduka ya kai mu mako na gaba zamu dora. NAGODE.