NOMAN WAKEN SUYA
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu na noma da kiwo inda muke tattaunawa akan al'amuran da suka shafi noma da kiwo don bunkasa tattalin arzikin al'umarmu,yankinmu da kuma kasarmu baki daya. A wannan makon da yardar mai-duka zamu tattauna akan noman waken suya. Da fatan masu karatu za'a kasance damu.
GABATARWA
Waken suya na daya daga cikin amfanin gona da aka sansu tun da dadewa a can nahiyar ASHIYA (Asia), wanda suke noman sa dan samar da mai,madara da kuma sauran sinadaran kara kuzari irin su PROTEIN da sauran su. Ana noman waken suya ne a waje mai yanayin zafi. Ainihin manoman waken suya kamar yadda binciken masana ya nuna suna noman shine don samar da takin gargajiyya sakamakon yawan sinadarin nan na NITROGEN da yake kunshe dashi. Musamman ga manoma masu yin noman kewaye wato (crop rotation) inda ake shuka shi a matacciyar gona bayan ya fito sai su bi shi da kasa su binne daga baya kuma sai a shuka amfani.
Cigaban da aka samu na fasahar zamani ta hanyar sarrafa da adana man waken suya yasa aka samar da hanyoyin amfani dashi daban-daban, wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna akan abin da ya shafi tarihi,asali da cigaban da aka samu a duniya wajen noman waken-suya,wannan ya kunshi nomansa,cututtuka da kwarikan dake addabarsa da yadda za'a magancesu,yadda ake zuba taki da girbinsa da yadda manomi zai adana shi, da kuma uwa-uba yin tsokaci kan irin muhimmiyar gudummawar da waken-suya ke bayarwa wajen cicciba tattalin arzikin duniya.
TAKAITACCEN TARIHI
Kamar yadda muka fada, yankin Ashiya (Asia) shine yanki na farko kamar yadda masana suka fada da aka fara noman waken-suya,wanda suke noman sa a matsayin dangin furannin dajin nan da ake kira da (Glycine soja) kusan shekaru 5000 da suka gabata. Duk da haka, asali da tarihin noman waken-suya ba zai cika ba tare da ambaton wannan shararren jarumin nan na kasar Sin (China) wato SHENNONG wanda akewa lakabi da ''DIVINE FARMER'', masana tarihi sun tabbatar da cewa oshine wanda ya kawo fasahar noma ga mutanen kasar Sin da kuma Biyatnam (Vietnam), ance ya sanya wken-suya a cikin furannin daya kira ''Tsarkakakkun furanni guda biyar'' wanda suka kunshi shinkafa,alkama,dawa da kuma gero. Hakanan a shekara ta 1000 kafin haihuwar Annabi Isa aka fara noman waken-suya a kasar Jafan (Japan) da Koriya (Korea) wato tun a zamanin mulkin Rumawa.
Waken-suya yana daga cikin dangin Legum wanda ya hada da wake da sauran su. Wannan dangi shine na uku mafi girma a dangin furannin kallo, dake dauke da dangi kala-kala har kusan 15,000. Waken-suya a kewaye yake yana dauke da launin ruwan dorawa-dorawa. Saboda yawan maikon da yake dashi da kuma sinadarin PROTEIN daya kunsa yasa akan iya sarrafa waken-suya ta hanyoyi daban-daban domin amfani iri-iri.
Masana tarihi sun tabbatar da cewa noman waken-suya ya bulla a nahiyar turai da kasar Amurka tun a lokacin mulkin mallaka. Hakanan manoman yankin Ashiya sun fara noman waken-suya ne ka'in da na'in a shekarar 1910. Tun daga sannan noman waken-suya ya habbaka a wannan yanki, inda a halin yanzu kasar Amurka ke jagoranta da kashi 55 cikin dari wato (55%) yayin da idan muka dawo yankin mu na Afirika kuma kasarmu ce ta Najeriyya ke jagoranta yayin da kasar Afirika ta kudu (South-africa) ke rufa mata baya.
Da yardar mai-duka zamu dora a mako na gaba. NAGODE
No comments:
Post a Comment