NOMAN AUDUGA 2
NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA
Masu karatu da fatan kuna tare da mu kuma kun ji dadin mukalar mu ta makon da ya gabata , a yau da yardar mai duka muna dauke da karashen wannan mukala da muke tattaunawa akan noman auduga.
Noman auduga a Najeriyya musamman ma a wannan yankin namu yafi karkata da yin amfani da katti yayin da a sauran sassan duniya ake amfani da taraktocin noma da injina da saukaka wa da kuma saman amfani mai yawa. Auduga na tsananin bukatar ruwa tare da magungunan kashe kwari (wanda binciken masana ya tabbatar da akwai jinsinan kwari sama da 1300, ciki wanda 500 suna wannan nahiyar tamu ta Afirika da suka dogara da auduga dan samun abinci) da kuma wadataccen taki. Bisa ga haka ne ma kasashen Amurka da Hindu wato (India) suka samar da wanisabon irin auduga wanda suka sauya fasalinsa ta hanyar binciken kimiyya wanda suke kira da (Genetics) ko (Genetically modified cotton) ko (GM) a takaice. GM cotton na da tsananin juriya daga kwari da rashin ruwa da kuma sauran cututtuka. Dadin dadawa kuma kwari basa iya cin sa saboda dafin dake tare da shi.
Auduga na bukatar lokacin noma mai tsayi, kasa mai yawa, da haske ga kuma uwa-uba ruwa wanda ake bukatar akalla zira'i biyu, binciken masana harkar noma suntabbatar da saboda bukatar ruwa da auduga ke bukata ya zama silar kwararowar hamada a yankunan tsohuwar tarayyar sobiyat wato (U.S.S.R). A halin yanzu kasar Amurka da sauran kasashen nahiyar Afirika ke jagorantar noman auduga a fadin duniya.
Najeriyya ma ba'a barta a baya ba wajen noman auduga, a matsayinta na daya daga cikin ginshikan ci gaban tattalin arzikin wannan kasa da kuma samar da kudaden shiga tun daga hshekarar 1903 zuwa yau. A kokarin gwamnati na ganin ta bunkasa wannan harka ta noman auduga yasa ta kafa hukumomi da kwamitoci daban-daban don bada shawara kan yadda za'a bunkasa wannan harka. Wadannan hukumomi da kwamitoci siun hada da British Cotton Growers Association, har ya zuwa shekarar 1974 inda aka maye gurbin ta da Cotton Marketing Board. A sabili da tsarurrukan gwamnati na sauya fasalin tattalin arzikin wannan kasa yasa gwamnati ta rushe wannan hukuma tare da dakatar da ayyukanta tare da kafa wani kwamitin tuntuba a madadinta wanda ta kira da Cotton Consultative Commitee (CCC). Wannan bai tsaya anan ba a shekara 2005 an sake kafa wani kwamiti mai suna Cotton Development Commitee wanda aka dora alhakin farfado da noman auduga ta hanyar amfani da fasahar zamani don cigaban kasa.
NAHIYOYIN NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA
Duk shekara a noma auduga a abin da ya aki kadada sama da miliyan 0.2-0.6 inda tsaunukan Savannah ke jagorantar kaso mafi yawa. A shekarar 2007-2008 kawai an noma akalla tan 400,000 na irin auduga a kadada miliyan 0.3. Noman auduga a Najeriyya ya kasu izuwa manyan shiyoyi guda uku sune: shiyyar arewa ke da kashi sittin cikin dari (60%), shiyyar gabas nada kashi talatin cikin dari (30%), yayin da shiyyar kudu keda ragowar kashi goma cikin dari (10%). Kananan manoma masu gona mai girman kadada 3-5 ne suka mamaye noman auduga a najeriyya.
KAMMALAWA
A karshen wannan mukala ba zamu gajiya kan kira ga mutane da gwamnati kan wajibcin mu na koma da rungumar harkar noma ka'in da na'in domin cicciba tattalin arzikin kasarmu. Gwamnati na da kyakykyarawar da zata taka wajen bunkasa noman auduga ta hanyar tallafawa manoman auduga da kuma karfafawa masu zuba jari kan masana'antun samar da tufa a Najeriyya wadda ita ce masa'anta ta uku wajen tallafawa tattalion arzikin wannan kasa in ka cire danyan man fetur (crude oil) da noma sai masana'antun tufafi wato (textile industries) wanda suka dogara kacokan kan auduga dan yin ayyukan su. Sai mun hadu a mako na gaba. NAGODE
No comments:
Post a Comment