NOMAN AUDUGA
Masu karatu inai muku sallama tare da fatan alkhairi da kuma jinjina dan gane da jumurin karatu da kuma fatan alherin da kuke mana tare da kuma neman afuwar ku dangane da shirun da aka ji na yan kwanaki, wannan kuwa ya faru ne saboda tutsun na'ura da muka fuskanta, da fatan za'ai mana afuwa kuma a cigaba da kasancewa damu.A yau zamu tattauna kan abin da ya shafi noma da kasuwancin auduga a kasarnan.
Auduga na daya daga cikin kayan amfani gona da ake sarrafa su dan amfani iri daban-daban, wanda ya hada da sarrafa auduga don samar da tufafin sawa,samar da takardu,samar da magani,samar da mai da sauran kayan abinci. Auduga ana noman ta a ko'ina cikin fadin duniyar nan tamu, yayin da musayar kasuwancinta a kasuwar duniya ya kai sama da Dala biliyan 12 a duk shekara inda kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirika ke jagoranta da kaso mafi rinjaye. Wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna takaitaccen tarihin auduga,ire-iren ta,kasuwancinta,noman ta a yau da kuma bayanin yadda ake sarrafata don amfanin mu na yau da kullum.
TAKAITACCEN TARIHI
Auduga ko Al-qutn da yaren Larabci (Arabic), na daya ga cikin dangin furannin fulawoyin kallo wato (flowering plant). Akwai sanannun ire-iren auduga guda hudu. Akwai wadda ake kira da GOSSYPIUM HIPSUTUM wadda aka fi noman ta a kasashen Amurka,Mexico da kasashen karebiyan (carrebian).Sauran sun hada da TREE-COTTON wadda aka fi noman ta a kasashen Hindu (India) da Pakistan, sai BARBADEBSE ta kasashen kudancin Amurka da kuma LEVANTINE wadda ake noman ta a kasashen Afirika da kuma kasashen gabas ta tsakiya wato (Middle -east).
Masana tarihi sun tabbatar da an fara noman auduga kusan shekaru 6000 da suka gabata, a daular Harrafawa (Harapan) da ke yankin Asiya (Asia), daga nan noman auduga ya bazu,ya yadu zuwa fadin duniya inda Manoma suka dukufa ka'in da na'in wajen nomanta gwargwadon irin yanayin da Ubangiji ya hore musu.
AMFANIN AUDUGA
Auduga na da matukar amfani ga dan-adam ta yadda masana suka tabbatar da cewa matukar mutane zasu rayu to tilas suyi noman auduga. Domin kuwa baya ga amfani da auduga da ake yi don saka sutturun sawa, hakanan ana amfani da ita danyin zaren lilo,ragar kamun kifi,likkafani da sauransu. Saboda yawan alfanu da juriya da biyan bukata na auduga yasa masana'antun tufafi suka dogara kacokan kan auduga don biyan bukatun su.
Kazalika ana amfani da auduga dan magani,abinci da kuma samar da takardu. Kwallon auduga ana amfani dashi wajen dafa abinci sannan kuma naman ta akan ba dabbobi su ci.
Idan maiduka ya kai mu mako na gaba zamu dora. NAGODE.
No comments:
Post a Comment