Monday, 7 October 2013

    NOMAN WAKEN-SUYA 2

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka wanda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo da kuma yin bincike mai zurfi akan wannan harka ta noma da kiwo da kuma tsokaci kan hanyoyin zamani domin amfanin manoman mu na karkara da masu sha'awar shiga wannan harka don cicciba tattalin arzikin kasarmu da al'ummarmu. Idan masu karatu suna tare damu a wancan makon mun fara tattaunawa ne akan noman waken-suya da yardar mai-duka zamu dora. Allah kadai muke roko da yai mana jagoranci akan dukkanin al'amuranmu.

WAKEN-SUYA : ABINCI


Waken-suya na daya daga cimakar dan-adam masu gina jiki da sanya kuzari, musamman in mukai kyakykyawan duba na tsanaki da kuma kuma nazari kan muhimman sinadaran gina jikin nan da ke kunshe a cikin waken-suya:kamar yadda binciken masana ya nuna kaso 40 cikin 100 (40%) na waken-suya na kunshe da sinadarin furotin (protein), kashi 35 cikin 100 (35%) na kunshe da sinadarin kabohaidiret (carbohydrate), kashi 20 cikin 100 (20%) na kunshe da mai wato (fat oil) yayin da ragowar kashi 5 cikin 100 (5%) na waken-suya ke kunshe da sinadarin Ash (ash). Binciken masanan bai tsaya anan ba inda ya tabbatar da cewar waken-suya na daya daga cikin tsirarun amfanin gona da suke bada cikakken adadin da jiki yake bukata na sinadarin furotin, wannan shine dalilin da yasa ake amfani dashi sau da yawa a maimakon Nama da Madara.


Wannan yasa kamfanunuwan abincin gwangwani irin su MORNINGSTAR FARMS masu yin cincin din nan na humburger da sausage da sauran su ke amfani da waken-suya domin dandano mai armashi da gina jiki. Dalilin haka ne  ya sanya yawancin cimakar mutanen cana (china), Koriya (Korea), Japan (Japan) da kuma kudu-maso-gabashin Ashiya zaka samu akwai waken-suya. Hakanan kamfanunuwan yin madara ma ba'a barsu a baya ba wajen yin amfani da waken-suya domin yin madarar waken-suya da sauransu. Kazalika a wannan yanki namu ma akan sarrafa waken-suya domin yin Awara da sauran abinci masu gina jiki. A takaice dai waken-suya akan iya sarrafa shi nau'i daban-daban daya hadar da yin mai, garin fulawa da kuma abinci na dan-adam ko na dabbobi.




WAKEN-SUYA: AMFANI
A wadansu kasashen kamar su Amurka da nahiyar turai sun dogara da man waken-suya domin dafe-dafen abinci. Kazalika waken-suya ma ya samu kyakykyawar kulawar masana  kamar sauran amfanin gonakin damu ka tattauna inda masana kan kimiyyar noma sukai dogon bincike tare da fitar da wani nau'i na waken-suya wanda suka sauya halittar sa da ake kira da GENETICALLY-MODIFIED SOY wanda a takaice ake kira da (G.M.O).   G.M.O an fitar dashi domin manoman waken-suya, yana da juriya daga kwari gashi baya bukatar wani taki ko noma mai yawa. Wannan dalilin yasa manoman waken-suya sukai amanna dashi inda kashi 8 cikin 100 (8%) na manoman waken-suya ke amfani dashi a shekarar 1997 zuwa kashi 92 cikin 100 (92%)  a halin yanzu (2012).

Kazalika waken-suya yana taka muhimmiyar rawa game da kariya ga lafiyar dan-adam, musamman kasancewarsa magani kafiyan ga matsananciyyar cutar nan ta Daji wato (Cancer) da sauran cututtuka masu kama da haka, wannan binciken yazo ne akan maganganun da ake yadawa kan cewar waken-suya yana kawo cutar daji. Baya ga haka  akan shafa man waken-suya ga fatar jiki domin samun  kariya  daga  cizon sauro,kwarkwata, kudin-cizo da sauran miyagun kwarirrika.





WAKEN-SUYA: NOMANSA


Kamar yadda muka fada kasar  Amurka itace a gaba duk fadin duniya wajen noman waken-suya inda kasar Barazil wato (Brasil) ke mara mata baya yayin da kasar mu Najeriyya ke jagoranci a nahiyar Afirika (Africa) inda kasar Afrika-ta-kudu wato (South-africa) ke mara mata baya , duk da cewa a yan kwanakin nan alkaluman yawan adadin noman waken-suya na yin kasa a can kasar ta Amurka sakamakon karanci filaye da gonakin noma. A shekarar data gabata (2012) kawai an girbe Tan miliyan 224.2 (224.2 million metric ton) na waken-suya inda akwai kyakykyawan tsammanin nan da yan shekaru masu zuwa yawan waken-suya  da ake nomawa a duniya  zai kai Tan miliyan 280 saboda yawan bukatarsa a kasuwannin duniya. Idan muka dawo yankinmu kuma na Afirika kuma zamu ga ana noma abin da ya kai tan miliyan 1.8 na waken suya duk da yawan wannan adadi kasashen Afirika na shigo da abin da yakai tan 20,000 na waken-suya daga kasashen ketare.

Noman waken-suya dan kasuwancinsa a kasuwar duniya, kasashen Zambia,Zimbabwe da kuma Afrika-ta-kudu na kan gaba inda suka ware tafka-tafkan gonaki domin gudanar da wannan harka. Amma akasarin manomanmu na noman waken-suya na noman  don ci a gida, inda suke nomansa yawanci tare da Dawa,Gero,Rogo da sauransu.

Anan zamu dakata sai mai-duka ya kai mu mako na gaba inda zamu tattauna kan noman-waken suya a kasarmu Najeriyya musamman ma a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa. NAGODE.

No comments:

Post a Comment