NOMAN WAKEN-SUYA 3
waken-suya na daya daga cikin manyan amfanin gona na kan gaba da ake sarrafa su a masana'antu da kuma samar da abinci a wannan kasa ta Najeriyya. A kan iya noman waken-suya yayi kyau a cikin jahohi 36 hade da birnin tarayya na wannan kasa ba tare da bukatar wani taki mai yawa ko maganin feshin kwari ba. Waken-suya ya samu habbaka a wannan kasa saboda amfaninsa ga tattalin arzikin wannan kasa . Kuma shine kan gaba wajen samr da wadataccen man girki a kasuwannin duniya. Kamar yadda muka fada a baya waken-suya na kunshe da kashi 40 cikin 100 (40%) na sinadarin furotin (Protein), waken-suya ne kan gaba kan kowace irin cimaka ta dan Najkeriyya irin su sauran amfanin gona ko dabba ko tsuntsaye dake dauke dake dauke da adadin mai yawa na sindarin furotin. Kazalika irin waken- suya na kunshe da kashi 20 cikin 100 (20%) na busashshen mai.
Wani binciken masana ya tabbatar da cewa bunkasar da aka samu wajen kiwon kaji,talo-talo,kifi da sauransu a yan shekarun da suka gabata ya sanya karin bukatar waken-suya a kasuwannin wannan kasa. Binciken kuma ya tabbatar da cewa noman waken-suya ya kara habbaka a wannan kasa saboda yawancin manoman mu sun samu wayewa da kuma amsa kiraye-kiraye da hukumomi keyi domin rungumar noman waken-suya wanda alfanunsa bai tsaya kawai domin ci ko sayarwa ba kawai, a'a saboda muhimmancin sa wajen karawa kasar noma tagomashi ga kasar noma da aka noma shi akai. Dadin dadawa kuma kasuwannin waken-suya na dada habbaka kullu yaumun a wannan kasa tamu, yayin da manoman mu kuma dama ta samu nasamun abin kaiwa bakin salati.
ABUBUWAN LURA KAFIN A SHUKA IRIN WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.
Yanayi mai kyau da kuma kasar noma ingantacciya suna da tasiri sosai wajen samun amfani mai yado. Waken-suya yana yin kyau a dukkan yankunan wannan kasa wato yanki kudanci da kuma arewaci, inda yawan adadin ruwan sama yakai alkaluma 700 na ma'aunin (mm). Hakanan lokacin da yafi kamata manoma su shuka wakaen-suya ya ta'allaka da yanayi da kuma wajen da za'a noma waken-suya. Manoman waken-suya a najeriyya na iya noma shi a kowace gona da dandananta ya kai lissafin alkalami 4.5 zuwa 8.5 na ma'aunin (ph). ya kamata manoman waken-suya su lura da cewa ba'a noman waken-suya a gona mai yashi,ko ma tarin duwarwatsu, ko mai kwari ko kuma mai hyawan kwazazzabai.
KIN TSA GONA KAFIN SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.
(1) SHARAR GONA :
Ana bukatar a kau da dukkanin ciyayi kafin shuka waken-suya. Ramin iri kuwa za'a iya shirya shi ta hanyar amfani da fatanya, ko garmar shirya ko kuma ta yin amfani da motar tarakta (Tractor). A kula da cewa gonar da aka kintsa ta sosai don shuka waken-suya ko kowanne irin amfanin gona yana tabbatar da saurin yin tsiro da kuma rage tasirin ciyayi a cikin gona. Hakanan manomi zai iya shuka irin waken-suya a kan kunya koma ba'a kunya ba.
(2) ZABEN IRIN NOMA:
A kowanne lokaci manomi ya tashi zaben irin noma ba kawai na waken-suya ba, ya tabbatar ya zabi irin da ya dace da yanayin yankin da yake. Zabin irin noman waken-suya, wajibi ne ya zama kan saurin yin tsiro, yawan yado, juriya daga fari ko kamfar ruwa da kuma jajircewa kwari da sauran cututtuka masu addabar waken-suya. Wajibi kuma manomi ya lura da cewa lokacin nunar irin waken-suya shine farkon abin lura wajen zaben irin waken-suya da ya dace da yankinsa.
Yana da kyau manomi ya zabi irin waken-suya mai saurin nuna kan wanda kan wanda baya nuna da wuri a wajen da yake da karancin ruwa ruwa. Duk da cewa wadansu manoman suna ganin noman irin waken suya mai dogon zango (wanda baya nuna da wuri) yafi yado, amma fa tabbas ya kamata manoman mu na waken-suya su fahimci iri hadarin da yake tattare da noman waken-suya mai dogon zango a yankin da yake da kamfar ruwan-sama saboda tsoron fari.
(3) GYARA IRIN WAKEN-SUYA DA SHIRYA SHI A NAJERIYYA:
Shawarar mu ga manoman mu na waken-suya shine a kullum kuyi amfani da iri mafi inganci wajen shuka, saboda irin waken-suya nan da nan yake rasa karsashin sa. Wannan kamar yadda muka sani gama-garina, domin kuwa waken-suya koda ammasa ajiya mai kyau ba zai yi tsiro ba bayan wata 12 zuwa 15 na ajiya. Saboda haka yana da kyau manoman mu su zabi Irin waken-suya da bai kai wata 12 da ajiya ba. Yana da kyau manomi ya zabi Iri masu kyau daya tabbatar ba kwaron daya kusance su, ko wata cuta, ko kuma yana hade da wani Iri na ciyawa. Manomi kada ya sai Iri a cikin kasuwa wanda bashi da tabbas na ingancin Irin, domin kuwa shuka Iri mara kyau ba zai ba da amfani mai yado ba. A koda yaushe monomi ya tabbatar ya sai Irin waken-suya a kamfanunuwan da suke sai da Iri ko kuma masu sarrafa Irin waken-suya da suke kusa da ku.
Da yardar mai-duka zamu dora in Allah tabaraka wa ta'ala ya kai mu mako na gaba. Kuma ina godiya da sakonnin fatan alkhairi da nake samu daga gareku, da fatan Allah ya saka muku da alkhairinsa. NAGODE.
No comments:
Post a Comment