Monday, 21 October 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (4)

NOMAN WAKEN-SUYA  (4)


Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka na noma da kiwo inda muke tatttauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo musamman a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa domin ganin mun ba da gudummawa wajen cicciba tattalin arzikin wannan yanki namu da kuma kasar mu baki daya.

wannan dandali na taya ku  murnar barka da babbar sallah da fatan Allah ta'ala ya karbi ibadun mu da yankanmu. Wannan dandali kuma yana mai addu'a ga  alhazan mu  da suke can kasa mai tsarki (Makka) domin gudanar da ibadar aikin hajji Allah ta'ala ya karbi ibadunsu kuma  ya dawo  mana su gida lafiya.  Amin


GWADA KARFIN IRIN WAKEN-SUYA

Yana da kyau manomi ya tabbatar kafin ya kai ga shuka irin waken-suya ya tabbatar ya jarraba irin domin ta hanyar hakane zai iya gane ko irin da zai amfani dashi mai kyau ne kuma mara kyau ne. Idan ya samu kashi 85 cikin dari (85%) na irin da ya shuka sun yi tsiro to mai kyau ne, manomi zai iya shuka wannan irin. 

Yadda manomi zai iya ganewa cewa irin sa mai kyau ne kuwa shine ya debi iri akalla guda 400 sai ya kasa su gida hudu ya shuka a wajen daya tanada domin gwajin iri, inda zai  kasa wurin  zuwa gida hudu ya shuka kowanne iri 100 a waje daban. Zai shuka kowanne iri ta hanyar ba da tazarar santimita (centimetre) 10 a tsakani. Ya tabbatar yana zuba isasshen ruwa safiya da maraice (yammaci).  Manomi kan  iya fara kirga irin da yai tsiro daga kwana biyar zuwa kwana goma, daga nan  inya samu tsiro 320 ko sama da haka (wanda ya kai kashi 80 cikin 100 (80%) kenan ka sama da haka) zai iya shuka wannan irin tare da kyakkyawar fatan samu amfani mai yawa.

             SHUKA WAKEN-SUYA

LOKACIN SHUKA

A kan iya shuka waken-suya a lokaci daban-daban, domin kuwa wannan ya ta'allaka da yanayin wajen da manomi yake kamar yadda  zami bayani nan  gaba kadan da yardar mai-duka. Dan haka ba'a son manomi ya shuka waken-suya da wur-wuri tun gabanin ruwan sama ya kan-kama don yin hakan zai iya zama aikin baban giwa inda zai zame wa manomi aiki biyu don kuwa sai ya sake shuka   wani irin.  Kazalika ba'a son yin jinkiri wajen shuka waken-suya, domin jinkirin zai iya kawo kwari da sauran munanan cututtuka da zasu iya  ragewa amfani karsashe. Saboda haka ana bukatar manomi ya shuka irin waken-suya daga  lokacin da ruwan sama ya kan-kama.


ADADIN IRIN WAKEN-SUYA DA AKE BUKATA

Idan manomi ya shuka kilo 50 zuwa 70 na irin waken-suya akwai kyakkyawar yiwuwar samun tsirrai dubu dari hudu da dari hudu da arba'in da hudu wato (444,444) a kowacce kadada guda. Amma tun da irin waken-suya ya banbanta daga girma  zuwa girma (inda  zaka samu iri na waken-suya guda 100 ya kai nauyin giram 12.6 wani kuma ya kan kai giram 18.9).

TUFATAR DA IRI
Yana da kyau ga kowanne manomin waken-suya ya tabbatar  kafin ya kai ga shuka irin sa ya tufatar dashi da magungunan cututtuka da kuma kwari. Manomi kan iya amfani da sanannen maganin nan na APRON PLUS ko THIAM. Duk jaka daya wato (sachet) a cakuda shi a cikin iri  daya kai kilo takwas kafin shuka domin samun kariya daga cututtukan dake  addabar waken-suya a cikin  gona.

YADDA AKE SHUKA WAKEN-SUYA DA KUMA TAZARAR DA YAKAMATA MANOMA SU BARI.

Manomi kan iya shuka ta hanyar yin  amfani  da hannu  ko kuma abin shuka. Manomi ya  shuka waken-suya  guda uku zuwa hudu  a kowanne rami, kana ya  bada tazarar santimita (Centimetre)  75 a kwance da kuma santimita 10 a tsaye.  Amma  ga irin waken-suya mara dogon-zango manomi kan  iya  shuka  shi ta  hanyar barin tazarar santimita  50 a kwance da kuma santimita 5 a tsaye, saboda kasancewar iri  waken-suya mara dogon-zango sun fi jin dadin tazara mai kunci ba kamar irin waken-suya  mai  dogon-zango ba.  Manomin waken-suya ya tabbatar ya kula sosai wajen ramin da zai zuba irin waken-suya kada zurfin ya kai santimita biyu zuwa biyar.  Domin kuwa yin ramin da za'a zuba waken-suya  da zurfi ya kan iya hanashi yin  tsiro kwata-kwata.


LOKACIN DA AKA FI SON A SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.

Lokaci abin so bisa ga binciken masana don shuka waken-suya a Najeriyya ya kasu gida biyu.

(1) yankin da ake kira da GUINEA SAVANNAH- farkon watan yuni (July) zuwa watan yuni (July)

(2) yankin da ake kira SUDAN-SAVANNAH- tsakiyar watan yuni zuwa farkon watan yulin kowacce shekara.


Idan mai-duka ya kai mu mako na gaba zamu dora daga inda muka tsaya inda zamu tattauna akan shin ko waken-suya na bukatar TAKI?
NAGODE

No comments:

Post a Comment