NOMAN WAKEN-SUYA (5)
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo domin kara wayarwa da manoman mu da masu sha'awar shiga wannan harka ta noma da kiwo tare da yin tsokaci kan alfanun dake ciki, musamman ma a kokarin da muke domin bunkasa tattalin arzikin wannan kasa. Kamar yadda muka dau akalla fiye da wata guda muna tattauna abin da ya shafi noman waken-suya a yau da yardar mai-duka zamu dora daga inda muka tsaya a makon daya gabata.
WAKEN-SUYA: TAKI
Adadin yawan takin da gona ke bukata domin noman waken-suya ya ta'allaka da irin dandanan kasar da kuma yankin da gonar take. Kamar yadda mu kai tsokaci a baya kuma akasarin manoman waken-suya suka sani cewar waken-suya baya bukatar takin dake kunshe da sinadarin NITROGEN kasancewar da kansa yake samarwa kansa wannan sinadari, kuma kamar yadda binciken masana kimiyyar noma ya nuna waken-suya na dogara ne kacokan da sinadarin NITROGEN domin girma. Binciken kuma ya tabbatar da karancin sinadarin PHOSPHURUS a waken-suya don haka ake bukatar manomi da ya zuba taki mai dauke da wannan sinadari na PHOSPHURUS domin samun amfani mai yado. Ana bukatar manomi ya zuba sinadarin PHOSPHUROS da yakai adadin kilo 30 a duk kadada guda (hecter) ta hanyar amfani da takin da ake kira da (super phosphate fertiliser). Hakanan taki mai dauke da sinadarin NITROGEN da POTASSIUM ana zuba sune kawai a yayin da manomi ya fahimci karancin su kuru-kuru a cikin gona. A kan iya cakuda takin da ake son amfani dashi yayin yin sharar gona ko lokacin yin haro (Harrow).
NOMAN WAKEN-SUYA: TAGOMASHI
Kamar yadda muka fada a baya waken-suya na kara tagomashin gona ta hanyar sanya adadi mai yawa da gona ke bukata na sinadarin NITROGEN a cikin kasa. Musamman ma idan manomi ya shuka shi tare da masara (wadda in Allah ya yarda zamu tattauna akan noman ta nan gaba kadan) yana taimakawa gaya wajen kashe muguwar ciyawar nan da ake kira da stringa hermonthinca.
KWARIRRIKA DA CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA HANYOYIN MAGANCE SU A GONA.
CIYAYI DA YADDA ZA'A MAGANCESU
Ciyayin dake addabar waken-suya duk shekara ko kuma a shekara sau biyu , wato lokacin noman damina da kuma lokacin noman rani , sun fi addabar waken-suya yayin da yai tsiro ya dan fara girma. Don haka tashi tsaye ga manomi akan lokaci domin magance wannan matsala kan iya rage karfi da kuma tasirinta a jikin waken-suya. Manomi kan iya magance tasirin ciyayi a cikin gona ta yin amfani da hanyoyi guda biyu da zamu ambata, wato ko dai ta yin amfani da hanyar gargajiyya ko kuma ta yin amfani da hanyar zamani.
HANYAR GARGAJIYYA; anan ana bukatar manomi ya fara nome ciyayin da suka fito a cikin gona sati biyu bayan shuka, sannan sai ya bari sai bayan sati na biyar zuwa shida da yin shuka ya kara yin wata nomar. Yana da kyau manomi ya kiyaye yin gaggawa wajen yin noman ciyayin gona tun kafin ruwan sama ya kan-kama domin yin hakan zai iya zama yin aikin baban giwa. Hakanan yin noman ciyawa mara kyau ko kuma dogon jinkiri wajen nome ciyayi zai iya rage yawan amfanin da za'a samu in girbe waken-suya.
HANYAR ZAMANI; anan ana bukatar manomi yai amfani da magungunan feshi don kashe ciyayin da suka fito yayin noman waken-suya. Magungunan feshin ciyayi suna da tasiri sosai in manomi yayi amfani dasu yadda ya kamata. Kazalika zaben magani kashe kwari daya kamata manomi yai amfani dashi a cikin gonar sa ya ta'allaka da iri yanayi ciyawar da ta fito da kuma saukin samun maganin a inda manomin yake. Duk da cewa magungunan kashe ciyayi suna nan a wadace ga ciyayin da basu bayyana ba dama wadanda suka bayyana a cikin gona. Don haka in aka fesa maganin kashe ciyayi a cikin gona, manomi zai fara nome ciyawa da zarar an shiga sati na biyar zuwa shida da shuka waken-suya a cikin gona.
Da yardar Allah mai kowa mai komai zamu kammala wannan mukala a mako mai zuwa. NAGODE.
Monday, 28 October 2013
Monday, 21 October 2013
NOMAN WAKEN-SUYA (4)
NOMAN WAKEN-SUYA (4)
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka na noma da kiwo inda muke tatttauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo musamman a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa domin ganin mun ba da gudummawa wajen cicciba tattalin arzikin wannan yanki namu da kuma kasar mu baki daya.
wannan dandali na taya ku murnar barka da babbar sallah da fatan Allah ta'ala ya karbi ibadun mu da yankanmu. Wannan dandali kuma yana mai addu'a ga alhazan mu da suke can kasa mai tsarki (Makka) domin gudanar da ibadar aikin hajji Allah ta'ala ya karbi ibadunsu kuma ya dawo mana su gida lafiya. Amin
GWADA KARFIN IRIN WAKEN-SUYA
Yana da kyau manomi ya tabbatar kafin ya kai ga shuka irin waken-suya ya tabbatar ya jarraba irin domin ta hanyar hakane zai iya gane ko irin da zai amfani dashi mai kyau ne kuma mara kyau ne. Idan ya samu kashi 85 cikin dari (85%) na irin da ya shuka sun yi tsiro to mai kyau ne, manomi zai iya shuka wannan irin.
Yadda manomi zai iya ganewa cewa irin sa mai kyau ne kuwa shine ya debi iri akalla guda 400 sai ya kasa su gida hudu ya shuka a wajen daya tanada domin gwajin iri, inda zai kasa wurin zuwa gida hudu ya shuka kowanne iri 100 a waje daban. Zai shuka kowanne iri ta hanyar ba da tazarar santimita (centimetre) 10 a tsakani. Ya tabbatar yana zuba isasshen ruwa safiya da maraice (yammaci). Manomi kan iya fara kirga irin da yai tsiro daga kwana biyar zuwa kwana goma, daga nan inya samu tsiro 320 ko sama da haka (wanda ya kai kashi 80 cikin 100 (80%) kenan ka sama da haka) zai iya shuka wannan irin tare da kyakkyawar fatan samu amfani mai yawa.
SHUKA WAKEN-SUYA
LOKACIN SHUKA
A kan iya shuka waken-suya a lokaci daban-daban, domin kuwa wannan ya ta'allaka da yanayin wajen da manomi yake kamar yadda zami bayani nan gaba kadan da yardar mai-duka. Dan haka ba'a son manomi ya shuka waken-suya da wur-wuri tun gabanin ruwan sama ya kan-kama don yin hakan zai iya zama aikin baban giwa inda zai zame wa manomi aiki biyu don kuwa sai ya sake shuka wani irin. Kazalika ba'a son yin jinkiri wajen shuka waken-suya, domin jinkirin zai iya kawo kwari da sauran munanan cututtuka da zasu iya ragewa amfani karsashe. Saboda haka ana bukatar manomi ya shuka irin waken-suya daga lokacin da ruwan sama ya kan-kama.
ADADIN IRIN WAKEN-SUYA DA AKE BUKATA
Idan manomi ya shuka kilo 50 zuwa 70 na irin waken-suya akwai kyakkyawar yiwuwar samun tsirrai dubu dari hudu da dari hudu da arba'in da hudu wato (444,444) a kowacce kadada guda. Amma tun da irin waken-suya ya banbanta daga girma zuwa girma (inda zaka samu iri na waken-suya guda 100 ya kai nauyin giram 12.6 wani kuma ya kan kai giram 18.9).
TUFATAR DA IRI
Yana da kyau ga kowanne manomin waken-suya ya tabbatar kafin ya kai ga shuka irin sa ya tufatar dashi da magungunan cututtuka da kuma kwari. Manomi kan iya amfani da sanannen maganin nan na APRON PLUS ko THIAM. Duk jaka daya wato (sachet) a cakuda shi a cikin iri daya kai kilo takwas kafin shuka domin samun kariya daga cututtukan dake addabar waken-suya a cikin gona.
YADDA AKE SHUKA WAKEN-SUYA DA KUMA TAZARAR DA YAKAMATA MANOMA SU BARI.
Manomi kan iya shuka ta hanyar yin amfani da hannu ko kuma abin shuka. Manomi ya shuka waken-suya guda uku zuwa hudu a kowanne rami, kana ya bada tazarar santimita (Centimetre) 75 a kwance da kuma santimita 10 a tsaye. Amma ga irin waken-suya mara dogon-zango manomi kan iya shuka shi ta hanyar barin tazarar santimita 50 a kwance da kuma santimita 5 a tsaye, saboda kasancewar iri waken-suya mara dogon-zango sun fi jin dadin tazara mai kunci ba kamar irin waken-suya mai dogon-zango ba. Manomin waken-suya ya tabbatar ya kula sosai wajen ramin da zai zuba irin waken-suya kada zurfin ya kai santimita biyu zuwa biyar. Domin kuwa yin ramin da za'a zuba waken-suya da zurfi ya kan iya hanashi yin tsiro kwata-kwata.
LOKACIN DA AKA FI SON A SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.
Lokaci abin so bisa ga binciken masana don shuka waken-suya a Najeriyya ya kasu gida biyu.
(1) yankin da ake kira da GUINEA SAVANNAH- farkon watan yuni (July) zuwa watan yuni (July)
(2) yankin da ake kira SUDAN-SAVANNAH- tsakiyar watan yuni zuwa farkon watan yulin kowacce shekara.
Idan mai-duka ya kai mu mako na gaba zamu dora daga inda muka tsaya inda zamu tattauna akan shin ko waken-suya na bukatar TAKI?
NAGODE

Monday, 14 October 2013
NOMAN WAKEN-SUYA 3
NOMAN WAKEN-SUYA 3
waken-suya na daya daga cikin manyan amfanin gona na kan gaba da ake sarrafa su a masana'antu da kuma samar da abinci a wannan kasa ta Najeriyya. A kan iya noman waken-suya yayi kyau a cikin jahohi 36 hade da birnin tarayya na wannan kasa ba tare da bukatar wani taki mai yawa ko maganin feshin kwari ba. Waken-suya ya samu habbaka a wannan kasa saboda amfaninsa ga tattalin arzikin wannan kasa . Kuma shine kan gaba wajen samr da wadataccen man girki a kasuwannin duniya. Kamar yadda muka fada a baya waken-suya na kunshe da kashi 40 cikin 100 (40%) na sinadarin furotin (Protein), waken-suya ne kan gaba kan kowace irin cimaka ta dan Najkeriyya irin su sauran amfanin gona ko dabba ko tsuntsaye dake dauke dake dauke da adadin mai yawa na sindarin furotin. Kazalika irin waken- suya na kunshe da kashi 20 cikin 100 (20%) na busashshen mai.
Wani binciken masana ya tabbatar da cewa bunkasar da aka samu wajen kiwon kaji,talo-talo,kifi da sauransu a yan shekarun da suka gabata ya sanya karin bukatar waken-suya a kasuwannin wannan kasa. Binciken kuma ya tabbatar da cewa noman waken-suya ya kara habbaka a wannan kasa saboda yawancin manoman mu sun samu wayewa da kuma amsa kiraye-kiraye da hukumomi keyi domin rungumar noman waken-suya wanda alfanunsa bai tsaya kawai domin ci ko sayarwa ba kawai, a'a saboda muhimmancin sa wajen karawa kasar noma tagomashi ga kasar noma da aka noma shi akai. Dadin dadawa kuma kasuwannin waken-suya na dada habbaka kullu yaumun a wannan kasa tamu, yayin da manoman mu kuma dama ta samu nasamun abin kaiwa bakin salati.
ABUBUWAN LURA KAFIN A SHUKA IRIN WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.
Yanayi mai kyau da kuma kasar noma ingantacciya suna da tasiri sosai wajen samun amfani mai yado. Waken-suya yana yin kyau a dukkan yankunan wannan kasa wato yanki kudanci da kuma arewaci, inda yawan adadin ruwan sama yakai alkaluma 700 na ma'aunin (mm). Hakanan lokacin da yafi kamata manoma su shuka wakaen-suya ya ta'allaka da yanayi da kuma wajen da za'a noma waken-suya. Manoman waken-suya a najeriyya na iya noma shi a kowace gona da dandananta ya kai lissafin alkalami 4.5 zuwa 8.5 na ma'aunin (ph). ya kamata manoman waken-suya su lura da cewa ba'a noman waken-suya a gona mai yashi,ko ma tarin duwarwatsu, ko mai kwari ko kuma mai hyawan kwazazzabai.
KIN TSA GONA KAFIN SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.
(1) SHARAR GONA :
Ana bukatar a kau da dukkanin ciyayi kafin shuka waken-suya. Ramin iri kuwa za'a iya shirya shi ta hanyar amfani da fatanya, ko garmar shirya ko kuma ta yin amfani da motar tarakta (Tractor). A kula da cewa gonar da aka kintsa ta sosai don shuka waken-suya ko kowanne irin amfanin gona yana tabbatar da saurin yin tsiro da kuma rage tasirin ciyayi a cikin gona. Hakanan manomi zai iya shuka irin waken-suya a kan kunya koma ba'a kunya ba.
(2) ZABEN IRIN NOMA:
A kowanne lokaci manomi ya tashi zaben irin noma ba kawai na waken-suya ba, ya tabbatar ya zabi irin da ya dace da yanayin yankin da yake. Zabin irin noman waken-suya, wajibi ne ya zama kan saurin yin tsiro, yawan yado, juriya daga fari ko kamfar ruwa da kuma jajircewa kwari da sauran cututtuka masu addabar waken-suya. Wajibi kuma manomi ya lura da cewa lokacin nunar irin waken-suya shine farkon abin lura wajen zaben irin waken-suya da ya dace da yankinsa.
Yana da kyau manomi ya zabi irin waken-suya mai saurin nuna kan wanda kan wanda baya nuna da wuri a wajen da yake da karancin ruwa ruwa. Duk da cewa wadansu manoman suna ganin noman irin waken suya mai dogon zango (wanda baya nuna da wuri) yafi yado, amma fa tabbas ya kamata manoman mu na waken-suya su fahimci iri hadarin da yake tattare da noman waken-suya mai dogon zango a yankin da yake da kamfar ruwan-sama saboda tsoron fari.
(3) GYARA IRIN WAKEN-SUYA DA SHIRYA SHI A NAJERIYYA:
Shawarar mu ga manoman mu na waken-suya shine a kullum kuyi amfani da iri mafi inganci wajen shuka, saboda irin waken-suya nan da nan yake rasa karsashin sa. Wannan kamar yadda muka sani gama-garina, domin kuwa waken-suya koda ammasa ajiya mai kyau ba zai yi tsiro ba bayan wata 12 zuwa 15 na ajiya. Saboda haka yana da kyau manoman mu su zabi Irin waken-suya da bai kai wata 12 da ajiya ba. Yana da kyau manomi ya zabi Iri masu kyau daya tabbatar ba kwaron daya kusance su, ko wata cuta, ko kuma yana hade da wani Iri na ciyawa. Manomi kada ya sai Iri a cikin kasuwa wanda bashi da tabbas na ingancin Irin, domin kuwa shuka Iri mara kyau ba zai ba da amfani mai yado ba. A koda yaushe monomi ya tabbatar ya sai Irin waken-suya a kamfanunuwan da suke sai da Iri ko kuma masu sarrafa Irin waken-suya da suke kusa da ku.
Da yardar mai-duka zamu dora in Allah tabaraka wa ta'ala ya kai mu mako na gaba. Kuma ina godiya da sakonnin fatan alkhairi da nake samu daga gareku, da fatan Allah ya saka muku da alkhairinsa. NAGODE.

Monday, 7 October 2013
NOMAN WAKEN-SUYA 2
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka wanda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo da kuma yin bincike mai zurfi akan wannan harka ta noma da kiwo da kuma tsokaci kan hanyoyin zamani domin amfanin manoman mu na karkara da masu sha'awar shiga wannan harka don cicciba tattalin arzikin kasarmu da al'ummarmu. Idan masu karatu suna tare damu a wancan makon mun fara tattaunawa ne akan noman waken-suya da yardar mai-duka zamu dora. Allah kadai muke roko da yai mana jagoranci akan dukkanin al'amuranmu.
WAKEN-SUYA : ABINCI
Waken-suya na daya daga cimakar dan-adam masu gina jiki da sanya kuzari, musamman in mukai kyakykyawan duba na tsanaki da kuma kuma nazari kan muhimman sinadaran gina jikin nan da ke kunshe a cikin waken-suya:kamar yadda binciken masana ya nuna kaso 40 cikin 100 (40%) na waken-suya na kunshe da sinadarin furotin (protein), kashi 35 cikin 100 (35%) na kunshe da sinadarin kabohaidiret (carbohydrate), kashi 20 cikin 100 (20%) na kunshe da mai wato (fat oil) yayin da ragowar kashi 5 cikin 100 (5%) na waken-suya ke kunshe da sinadarin Ash (ash). Binciken masanan bai tsaya anan ba inda ya tabbatar da cewar waken-suya na daya daga cikin tsirarun amfanin gona da suke bada cikakken adadin da jiki yake bukata na sinadarin furotin, wannan shine dalilin da yasa ake amfani dashi sau da yawa a maimakon Nama da Madara.
Wannan yasa kamfanunuwan abincin gwangwani irin su MORNINGSTAR FARMS masu yin cincin din nan na humburger da sausage da sauran su ke amfani da waken-suya domin dandano mai armashi da gina jiki. Dalilin haka ne ya sanya yawancin cimakar mutanen cana (china), Koriya (Korea), Japan (Japan) da kuma kudu-maso-gabashin Ashiya zaka samu akwai waken-suya. Hakanan kamfanunuwan yin madara ma ba'a barsu a baya ba wajen yin amfani da waken-suya domin yin madarar waken-suya da sauransu. Kazalika a wannan yanki namu ma akan sarrafa waken-suya domin yin Awara da sauran abinci masu gina jiki. A takaice dai waken-suya akan iya sarrafa shi nau'i daban-daban daya hadar da yin mai, garin fulawa da kuma abinci na dan-adam ko na dabbobi.
WAKEN-SUYA: AMFANI
A wadansu kasashen kamar su Amurka da nahiyar turai sun dogara da man waken-suya domin dafe-dafen abinci. Kazalika waken-suya ma ya samu kyakykyawar kulawar masana kamar sauran amfanin gonakin damu ka tattauna inda masana kan kimiyyar noma sukai dogon bincike tare da fitar da wani nau'i na waken-suya wanda suka sauya halittar sa da ake kira da GENETICALLY-MODIFIED SOY wanda a takaice ake kira da (G.M.O). G.M.O an fitar dashi domin manoman waken-suya, yana da juriya daga kwari gashi baya bukatar wani taki ko noma mai yawa. Wannan dalilin yasa manoman waken-suya sukai amanna dashi inda kashi 8 cikin 100 (8%) na manoman waken-suya ke amfani dashi a shekarar 1997 zuwa kashi 92 cikin 100 (92%) a halin yanzu (2012).
Kazalika waken-suya yana taka muhimmiyar rawa game da kariya ga lafiyar dan-adam, musamman kasancewarsa magani kafiyan ga matsananciyyar cutar nan ta Daji wato (Cancer) da sauran cututtuka masu kama da haka, wannan binciken yazo ne akan maganganun da ake yadawa kan cewar waken-suya yana kawo cutar daji. Baya ga haka akan shafa man waken-suya ga fatar jiki domin samun kariya daga cizon sauro,kwarkwata, kudin-cizo da sauran miyagun kwarirrika.
WAKEN-SUYA: NOMANSA
Kamar yadda muka fada kasar Amurka itace a gaba duk fadin duniya wajen noman waken-suya inda kasar Barazil wato (Brasil) ke mara mata baya yayin da kasar mu Najeriyya ke jagoranci a nahiyar Afirika (Africa) inda kasar Afrika-ta-kudu wato (South-africa) ke mara mata baya , duk da cewa a yan kwanakin nan alkaluman yawan adadin noman waken-suya na yin kasa a can kasar ta Amurka sakamakon karanci filaye da gonakin noma. A shekarar data gabata (2012) kawai an girbe Tan miliyan 224.2 (224.2 million metric ton) na waken-suya inda akwai kyakykyawan tsammanin nan da yan shekaru masu zuwa yawan waken-suya da ake nomawa a duniya zai kai Tan miliyan 280 saboda yawan bukatarsa a kasuwannin duniya. Idan muka dawo yankinmu kuma na Afirika kuma zamu ga ana noma abin da ya kai tan miliyan 1.8 na waken suya duk da yawan wannan adadi kasashen Afirika na shigo da abin da yakai tan 20,000 na waken-suya daga kasashen ketare.
Noman waken-suya dan kasuwancinsa a kasuwar duniya, kasashen Zambia,Zimbabwe da kuma Afrika-ta-kudu na kan gaba inda suka ware tafka-tafkan gonaki domin gudanar da wannan harka. Amma akasarin manomanmu na noman waken-suya na noman don ci a gida, inda suke nomansa yawanci tare da Dawa,Gero,Rogo da sauransu.
Anan zamu dakata sai mai-duka ya kai mu mako na gaba inda zamu tattauna kan noman-waken suya a kasarmu Najeriyya musamman ma a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa. NAGODE.

Subscribe to:
Comments (Atom)