Monday, 25 November 2013

TURAKU GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (2)

                                                         TURAKU GOMA SHA DAYA NA
                                                            CIN NASARA A HARKAR
                                                                NOMA DA KIWO (2)



(6) Yaya kana da dagiya kan al'amura? gudanar da harkar noma na da wahalar gaske, wanda wannan zai iya janyo wa mutum gazawa a wadansu lokutan. Saboda yawancin  mamallakan wannan harka sukan gaza wajen daukar nasara ko rashinta.  Don haka kana bukatar ka dunga samun karfafa gwuiwa a kowanne lokaci don cigaba da dorewar  wannan harka, da kuma kariya daga gurguncewar harkar da makamantansu. Domin kuwa da wannan harka tana da sauki gaya da kaga kowa   a cikin ta.  Anan ya kamata mu ari karin maganar nan da take cewa  idan kana son kayi sukuwar sallah a wannan harka ta noma da kiwo, dole ka zamto ka shirya faduwa daga kan dokin ka sau shurin masaki ba tare daka sare ba.


(7) Yaya harkar noma zai shafi iyalanka? Babu tantama cewar a farkon lokacin daka fara wannan harka  zai dan shafe ka da yarda kake gudanar da harkokin iyalanka ta bangaren  kudi.  Wannan kuwa  kan iya daukar watanni kai har shekaru ma kafin akai ga fara cin riba. Don haka wajibi ka shirya yadda zaka dan gyatta yadda kake gudanar da wadannan harkoki damin samun alheri mai yawa nan gaba kadan.


(8) Shin ka dau wadataccen lokaci kana nazari kan wannan harka don ganin ko akwai alheri a ciki kuwa? Kai sani zaka shiga harkar noma da kiwo ne da nufin samun alheri. Don haka kada kai gaggawa ba  tare daka shirya fuskantar kalubalen dake tattare  da wannan harka ba. Yana da kyau ka halarci tarurruka na karawa juna sani, sayen littafai na harkokin noma da kiwa da jaridu, mujallu da kuma mudawwanoni na wannan harka kamar dandalinnomadakiwo.blogspot.com.


(9) Shin kana da gogewa  kan irin harkar da zaka gudanar?  Yawancin wadanda suka cigaba sukai kaurin suna a wannan harka sun kasance suna da gogewa a wannan harka tun kafin sukai ga shiga cikinta ka'in da na'in. Ka halarci lakcoci kan wannan harka tun kan ka kai da fara wannan harka.


(10) Shin kana da karfin jari?  Rashin kudi   yawanci shine kashin bayan karya ko  gurgunta yawancin harkokin kasuwanci bawai kawai noma da  kiwo ba. Don haka kana  bukatar jari wadatacce domin gudanar da wannan harka yadda ya kamata.



(11) Shin kana iya sayarwa?  Kowanne  iri harkar kasuwanci na bukatar abokan hulda wato (customers) , wanda ake bukatar ka ka fara tuntuba tun farkon lokacin fara gudanar da wannan harka.  Yana da kyau kayi kokari kan bunkasa bangaren daya shafi saye da kasuwanci na wannan harka domin kuwa in dai hajarka bata karbu ba to kuwa wannan ya zama abin da ake kira anyi ba ai ba.



Da wadannan muhimman tambayoyi guda goma sha daya muke ganin duk wanda ya samu damar amsasu yadda ya kamata, zai shiga wannan  harka ta fatan samun nasara gwaggwaba na bada dadewa ba. Allah ya sanya albarka ya taimake mu akan dukkanin al'amuran mu na alkhairi kuma ya datar damu akan yin daidai. Da yardar mai-duka mako mai zuwa zamu tattauna abin da ya shafi kiwo.  NAGODE


3 comments:

  1. Assalamu alaikum,
    Alhamdulillah! Naji dadin ganin wannan rubuce-rebucen naka akan harkar noma. Allah ya biya ka akan wannan kokarin naka ya kuma kara ma hazaka. Na gode.

    ReplyDelete