Noman rani ko noman ban ruwa kamar yadda muka sani shine zuba ko sanya ruwa a gona ko kuma wata hanya ta gudanar da aikin gona ba tare da dogaro da ruwan sama ba ko zuwan damina ba kamar a wasu wuraren da suke da karancin ruwan sama ko ake samun yankewar ruwan sama a tsakiyar damina. Bayan wannan noman ban ruwa yana taimakawa wajen kara girman amfanin gona, kula da filin noma,sake rayar da filin noma musamman a lokacin rani.Amfanin noman ban ruwa ga amfanin gona ko da ita gonar kanta bai tsaya anan ba domin yana taimakawa wajen kare amfanin gona daga kwari,kassara ciyayin da suke fitowa a cikin gona, yana taimakawa gaya wajen hana zaizayar kasa a cikin gona, sannan yana ba da damar yin shuka fiye da sau daya a shekara.
TAKAITACCEN TARIHI
Noman ban ruwa kamar yadda dalilai na tarihi da binciken masana suka tabbatar abune mai dadadden tarihi musamman yankunan hamada da kuma yankunan da suke gabar koguna.Bincike ya tabbatar da shekaru masu yawa kafin haihuwar Annabi Isa ake noman ban ruwa a kogin nan na FURATA (AL-FURAT) dake aksar Iraki. A nahiyar afirika ma noman ban ruwa an fara shine a wajen karni na farko zuwa karni na biyu kafin haihuwar Annabi Isa wanda ya dogara ne da jan ruwa daga koguna kamar kogin nan na Nilu da sauransu.Amma samun cigaba na zamani da kuma shigowa injina masu aiki da man gas ko wutar lantarki wannan ya bunkasa harkar noman ban ruwa matuka gaya ta inda irin wadannan injinan tso-tso ruwa (pumping machine) sukan iya tso-tso miliyoyin lita na ruwa cikin takaitaccen lokaci.
Mizanin amfani da kayayyakin noman ban ruwa a duniya ya kai wajen kilomita 2,788,000 (wato eka miliyan 689) ta gonaki noma masu dauke da injinan ban ruwa a shekarar 2000. Inda wajen kashi 68 cikin dari na wadannan gonaki suna yankin ashiya ne inda kashi 17 yake ya ke a kasar Amurka,kashi 9 a nahiyar Turai yayin da kashi 5 cikin dari yake nahiyar mu ta Afirika.Inda aka fi noman ban ruwa a duk faduin duniya shine arewacin indiya da fakistan kusa da kogunan da ake kira da GANGES da INDUS. Binciken baya-bayannan da aka gudanar a shekarar 2008 ya nuna ana amfani da wajen kilomita 3,245,566 wanda ya kai kusan fadin kasar Indiya gaba dayanta.
Wadansu kamar yadda muka fada suna amfani da injina don ban ruwa a gona yayin da wasu kuma suke amfani da bokitai da butoci dan yi ban ruwa a gona da sauran hanyoyi masu yawa wanda in mun samu dama nan gaba zamu kara fadada bayani gamsashshe akai.Amma ya kamata mu sani cewa mu mun saba muna kiran irin wannan noma da noman rani a kasashe irin su Iran yawancin noman da a keyi ana yinsa ta hanyar ban ruwa a gona ko da kuwa a lokutan damina ne saboda karancin ruwan sama da suke fama da shi.Wani bincike da hukumar noma da abinci ta majalisar dinkin duniya ta wallafa a shekarar 1991 ya nuna a yankin Afirika ana amfani da kadada milyan 6 ne kawai wajen noman ban ruwa a cikin kadada miliyanm 40 da za'a iya wannan aiki dasu.Duk da haka zami kira ga gwamnatocimu kan su taimakawa manomanmu da injinan zamani na ban ruwa don kara yawan abincin da ake samarwa a wannan kasa.Sai mun hadu a mako na gaba. NAGODE.
Sunday, 27 May 2012
Friday, 18 May 2012
KAYAYYAKIN AMFANI A CIKIN GONA 3
Barkan mu da sake saduwa a wannan makon a wannan mudawwana tamu ta manoma mai albarka, idan mai karatu bai mantaba makonni biyu da suka gabata mun tattauna a wannan maudu'i namu na kayayyakin amfani a cikin gona (farm input) in da muka tattauna akan abin da ya shafi iri da taki inda wannan makon da yardar Allah zamu tattauna akan magungunan kashe kwari wato (pesticide) da kuma na kashe ciyawa wato (herbicide).
TAKAITACCEN TARIHI
Binciken masana tarihi ya tabbatar da cewa kimanin shekaru 2000 kafin zuwan Annabi Isa mutane sukan sarrafa wadansu sinadarai su samar da wadansu magunguna don su kare amfanin gonakinsu daga kwari. Farkon sanannen maganin kwari shine na sinadarin SULFUR wanda turawan daji wato (mesopotamia) suke amfani da shi wajen shekaru 4500 da suka gabata. Suma indiyawan THE RIG VEDA kimanin shekaru 4000 da suka shude suna amfani da wadansu ganyayyaki masu guba don kashe kwari.A karni na 15 ne aka kirkiro wadansu magunguna masu guba irin su ANSENIC, MERCURY da kuma LEAD ana fesa sune ga amfanin gona don su kashe kwari yayin da a karni na 17 ne sinadarin nan na NICOTINE SULFATE aka fid dashi daga ganyayyakin taba don kare amfanin gona daga cutarwar kwari. Binciken baya-bayannan ya nuna akwai sanannun sinadaran hada magungunan feshi wajen guda1,055 da kuma magungunan feshi masu rijista da suka haura 16,000. Amma maganin kashe ciyawa wato (herbicide) an fara amfani dashi ne a shekarar 1960 har zuwa yau.Saboda irin hadararrukan da yake cikin amfani da irin wadannan magunguna ne gwamnatoci su kan kafa dokoki kan amfani da irin wadannan magunguna ta hanyar hukumomi don su sa ido na ganin cewa anyi amfani da wadannan magunguna yadda ya kamata kuma bisa ka'ida.
BAYANI
Maganin kashe kwari wato (pesticide) ya kunshi sinadari ko hade-haden sinadarai domin su hana,su kashe,ko su zama kariya ga amfanin gona daga kwari.wannan kuwa ya hadarda cututtukan jikin bil'adama da dabbobi da ciyayi ko kuma dukkan wata halitta da take cutar da amfanin gona ko dabbobin kiwo; wajen nan zai iya zama cikin gona ne ko wajen sarrafa amfanin gona ne wato ma'aikata ko cikin Rumbu ne inda ake ajiyar amfanin gona ko a wajen safarar amfanin gona ne daga wani wuri zuwa wani wuri ko kuwa a wajen cinikayyar sune wato kasuwa. Maganin kashe kwari yana da fadi sosai domin kuwa yakunshi dukkan wasu sinadarai da aka sarrafa don hana kwari rabar jikin dabbobin kiwo. Hakanan dukkan sinadarin da akai amfani dashi don kula da girman yabanya,ko hana kayan marmari daga fadowa daga kan bishiya kafin su kai ga nuna. Kuma ya kunshi dukkan wani wadansu sinadarai da za'a sarrafa su ai amfani dasu kafin ko bayan girbi don ya zama kariya ga amfanin gona daga barnar kwari a lokacin ajiya ko a wajen safara.
Muhimmin amfanin wannan maganin kashe kwari a wajen akasarin manoman mu shine don ya zama mai bawa amfanin gonakin su kariya daga barnar kwari wadanda ake ganin macuta ne ko masu illah.Maganin kashe ciyawa wato (herbicide) kamar yadda muka sani ana amfani da shi ne don kashe ciyayin da ba'a bukatar su a cikin gona, amma yawancin manoman mu basu cika amfani da shi a cikin gonakinsu ba sai dai yawanci akan yi amfani da shine a wannan kasa wajen zubawa a cikin tafki ko rafi don kashe ciyayin da suke kawo tasgaro wajen ninkaya da kamun kifi sannan su jikirta launin ruwan zuwa launi mara kyan gani. Maganin kashe kwari akan yi amfani dashi a cijkin rumbu ko ma'ajiyar amfanin gona don ya hana kwari da suke bata abinci kamar hatsi da sauransu samun damar kaiwa garesu.Ya zama dole muja hankalin manoman mu wajen yin amfani da magungunan kashe kwari yayin ajiyar amfanin gona kan cewa ya zama wajiba su kiyaye dukkan wata ka'ida da kamfanin maganin ko hukumomin da suke sa ido kan wannan harka kamar NAFDAC suka gindaya kan amfani da wadannan magunguna saboda hadurran dake kunshe dasu.
Maganin kashe kwari yana taimakawa tattalin arzikin manomi nesa ba kusa ba domin wani bincike da aka aiwatar kwana- kwanan nan ya nuna kin yin amfani da maganin kashe kwari ga manomi a gona yana rage yawan amfanin gona da wajen kashi goma cikin dari.Hakanan wani bincike da aka aiwatar a shekarar 1999 lokacin da muhawara tai zafi akan hana amfani da magungunan kashe kwari saboda matsalolin da ake fuskanta daga manoma da yan kasuwa wajen kin bin cikakkiyar ka'idar amfani da maganin, sakamakon binciken ya nuna hana amfanin da wadannan magunguna zai kawo hauhawar kayan abinci, da rashin aikin yi, da kuma karuwar mizanin yunwa a duniya.Dangane da yanayin kasuwar magungunan kashe kwari kuwa kasuwar su a bude take domin wani biciken da aka gudanar a shekarar 2006 zuwa 2008 ya nuna duniya tana amfanin da wadannan magunguna da yakai na sama da naira tariliyan 1,300.
Amma duk da wannan karbuwa da wadannan magungunan su kayi bincike ya tabbatar da suna tattare da illoli masu yawa ga lafiyar dan'adam da kuma muhallinsa. Ta bangaren lafiya koya aka kuskure ya dan taba fata ko ido to wajen zai ta kaikayi wanda in ba' ai gaggawar daukar kwakwkwarar mataki ba zai iya kaiwa ga cutar daji wato (cancer). Binciken da hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya wato (W.H.O) ta gabatar ya nuna duk shekara akalla ma'aikatan feshin maganin kwari miliyan uku ne a kasashe masu tasowa ke kamuwa da cututtuka daga gubar dake tare da wadannan magungunan. Ta bangaren muhalli ma magungunan feshi ba'a bar su a baya ba domin bincike ya nuna a kalla kashi 98 cikin 100 na maganin feshi da ake fesawa a gona da kuma kashi 95 cikin 100 na maganin feshin ciyawa suna zuwa ne ba inda aka fesa suba wato sukan bi iska,ruwa da sauransu maimakon kisan kwari da ciyawa.
Amma wadannan illoli ko matsaloli baza su hana yin amfani da magungunan kashe kwari da ciyawa musamman duba da irin alfanun dake tattare dasu matukar ambi ka'ida kuma an tabbatar cewa kwararrun ma'aikata ne zasu gudanar da aikin to za'a samu alfanu masu yawa kamar haka ;kashe da hana yaduwar cututtuka a gona, karayawan amfanin gona masu inganci, bishiyoyi ma zasu samu kariya daga kwari kamar su Gara da sauran alfanu masu yawa da manoma zasu samu ta hanyar amfanin da wadannan magunguna a gona, Domin kuwa a duk naira daya da aka kashe don yin amfani da maganin feshi akan adana naira hudu ga bata daga kwari. Wannan yasa duniya tayi amanna da wadannan magunguna domin bincike ya nuna ana samun karuwar amfani da wadannan magunguna da wajen kashi 4 zuwa kashi 5.4 cikin dari a duk shekara.Nan zamu dakata sai kuma hadu a wani makon kafin sannan muna maraba da ra'ayoyin ku kan yadda muke gudanar da wannan mudawwana. NAGODE

Sunday, 13 May 2012
KAYAYYAKIN AMFANI A CIKIN GONA (FARM INPUT) 2
TAKI
Barkan mu da sake saduwa a wannan mako, waccan makon mun tattauna akan iri da nau'o'insa wannan mako in Allah ya yarda zamu yi bayani ne akan takwararsa wato Taki.Taki kamar yadda muka sani shine abinda shuka take sarrafawa ta mai dashi abinci.Binciken masana kimiyyar gona ya tabbatar da muhimmanci da gudummawar da taki yake badawa wajen bunkasa yabanya da kuma kariyar da yake bawa kasar gona daga lalacewa in anyi amfani dashi yadda ya kamata.Sai dai har yanzu akwai matsaloli nan da can wajen samar da taki mai inganci da kuma karancin ilimi ga manoma kan yadda zasu yi aiki dashi acikin gona.
GABATARWA
Binciken kimiyyar aikin gona ya tabbatar cewar kasa tana kunsheda sinadarai masu yawa wanda kwari suke sarrafawa domin samar wa kansu abinci.Wadatar wadannan sinadarai a kasa shine yake alamta karfin da kasa take dashi,wato dacewarta da rayuwar kwari da shuke-shuke. A sanadiyar noma kasa da ake da girbi har na tsawon wani lokaci wannan ya danganta da yanayin kasar wajen domin wata tafi wata karfi saboda sinadaran da suke kunshe a cikinta, ana nomata karfinta yana raguwa ahankali-ahankali ana gane haka ne kamar ta hanyar raguwar yawan amfanin gona da aka saba girba a kanta. To idan kasa ta kasance a irin wannan yanayi na rashin karfi,zaka ga su kansu kwari sun kasa samun isashshen abinci da suke bukata ballanrtana har su sarrafashi ya zama yabanya tai kyau. A irin wannan yanayi ne ake amfani da taki kona gargajiyya kona zamani domin dawowa da wannan kasa karfi da danko.
MENE NE TAKI
Taki shine wadansu sinadarai masu rai ne ko mara sa rai da ake sarrafawa, wanda ake zubawa akan kasa don a samu karin kuzari ga kasa ta yadda ita kuma yabanya zata bunkasa.Binciken da muka gabatar kwanan nan ya nuna wajen kashi 40-60 cikin dari na yawan abincin da ake nomawa ya ta'allaka ne kacokan kan amfani da taki a gona, domin karfin taimakon da yake bawa yabanya ta fuskar saurin girma da girbar amfani mai yawa.Hakanan binciken ya tabbatar da kasuwar taki a duniya zata kai sama da naira tiriliyan 3 daga nan zuwa shekarar 2018. Harsashe ya nuna wajen fiye da rabin mutanen duniya suna samun abincin da zasu cine ta hanyar wannan fasaha ta amfani da taki a gona.
YANAYI
Taki yana zuwa a nau'o'i da dama sananne shine ya zo a daskare kamar gari sannan yana zuwa a nau'in ruwa wanda yafi kowane nau'i cikin nau'i kan taki saurin game gona.
IRE-IREN TAKI
Akwai takin da ake sarrafawa ta hanyar ma'adanai wato takin da ake sarrafawa daga abubuwa marasa rai kamar sainadarin kanwa (potasium).Akwai kuma takin da ake sarrafawa daga abubuwa masu rai kamar su dabbobi da kwarika, da kuma abin da yak fitowa daga garesu kamar kashin su, da dai sauran abubuwa masu saurin rubewa. irin wannan taki shi ake kira da takin gargajiyya.
Takin zamani shi ya hada dangogi biyun, wato na ma'adanai da wanda ba na ma'adanai, wanda yawanci shi takin zamani ana sarrafa shine a masana'antu domin sayarwa ga manoma.
A karshe yawa da nau'in takin da ya kamata ai amfani dashi a gona ya dogara ne ga yanayin kasa da kuma nau'in amfanin da za'a shuka a wannan kasa. Malaman gona su kan yi gwaje-gwajen kasa ko yanki domin gane dangin taki da kuma yawan da kowane yanki ke bukata wannan dalilin ne yasa muke nanata kira ga manoma dasu dinga neman shawarwarin malaman gona kafin su kai ga zuba taki a gonakinsu. Wanda muma in Allah ya yarda duk amfanin gonar da muke bayani akansa zamu fadi nau'i da yawan takin da yake bukata in Allah ya yarda. Mako na gaba zamu dora

Sunday, 6 May 2012
KAYAYYAKIN AMFANI A CIKIN GONA (FARM INPUT).
A wannan makon da yardar mai duka zamu tattauna ne kan abin da ya shafi wajibai a cikin harkar noma wadanda inka cire gona ba wani abi da ya kai su muhimmanci a wannan sana'a ta noma. wadannan abubuwa da suka hada da Iri,Taki,Magunguna da kuma kayayyakin aiki na gargajiyya kamar su fatanya,magirbi da sauransu da kuma na zamani irin su motar tirakta da sauransu.Wadannan kayayyaki in anyi amfani dasu yadda ya kamata to shakka babu za'a samu amfani mai yawa kuma lafiyayye.
IRI
Iri shine dukkan wata kwaya ko tushe da aka shuka a kasa don a samu abinci ko amfani. Kaga kenan iri yana da matukar muhimmanci a harkar noma fiye da sauran yan'uwansa irin su taki da magani domin shi in ba 'a sa iri ba to ba maganar a girbi amfanin gona.Daga nan zamu fahimci cewa matukar ana so a samu wadataccen abinci da kayan sarrafawa a masana'antun mu da suka dogara da amfani gona wato (agro-allied industries) to abi na farko da za ai shine samar da ingantaccen iri kuma a wadace cikin saukin farashi.
Ana samun ingantaccen iri ta hanyoyi kamar haka a wannan zamani; ana samun ingantaccen iri mai nagarta da inganci ta hanyar binciken ilimin kimiyya wanda yawanci malaman kimiyyar aikin gona ne suke aiwatar da shi ta hanyar bin diddigi da dogon nazari da bincike na tsawan lokaci har su kai ga fitar ko samar da ingantaccen iri mai juriya kuma mai yalwa.Bayan wannan hanya manoma ma suna da wata dabara ko fasaha wajen fitar da ingantaccen iri shine sukan dau iri kaza na amfani kaza su gwada, a haka har su fitar da me kyau lafiyayye sa'annan su fitar da baragurbi.
Lallai indai ana so a samar da abinci mai yawa da inganci a wannan yanki namu da ma kasa baki daya to dole ne a samar wa manoman mu fasahar noma ta zamani a kuma dinga wayar musu da kai akan sababbin hanyoyin noma na zamani ta hanyar ilimintar dasu da basu shawarwari nagari. Hakanan dole a samar musu da irin noma na zamani kamar irin masara,tumatir,gero,alkama,rogo da sauransu wato nau'in abincin da mutanen yankin suka saba dashi.Cibiyar nan ta international institute of tropical agriculture (IITA) dake da mazauni a garin ibadan ta dade tana fitar da iri na zamani ga manoma. misali wani sabon iri da ta fitar na shinkafa na zamani wanda da in ka shuka irin da muka saba dashi a kadada 1 zaka girbi abin da baifi tan 2 ba na amfanin gona,amma wannan sabon iri inka shuka shi a kadada 1 zaka gibi amfanin gona da yakai tan 3-6 .Sannan ire-iren irin da ake shigowa dasu daga kasashen ketare kamar wani irin tumatir da aka shigo dashi daga kasar demmak zuwa najeriyya wanda manoman da suka gwada shi sun tabbatar da ingancin sa ta hanyar saurin nunarsa ga tsoka ga yalwa ga juriya da kuma girma.
A karshe mun gane muhimmancin iri a harkar noma tokuwa in hakane ya zama wajibi muyi kira ga gwamnatoci da su shigo cikin wannan harka ta samar wa manoma iri ingantacce domin ko a kasashen da suka cigaba irin wannan aiki sai manyan kamfanoni masu zaman kansu ne suke iya daukar dawainiyyar wannan aiki saboda daukar lokaci da kuma tsada.Kaga kenan in gwamnati ta shigo ciki zata tabbatar da fitar da wadataccen kudi da za'ai wannan aiki dasu,sannan tayi maganin matsalolin da manoma suke fuskanta inda suke asara yayin da suka sayi iri ba mai nagarta ba, kasancewar yawancin manoman wannan yanki namu masu karamin karfi ne to shigowar gwamnati ciki zai tabbatar da samar da iri mai inganci ga manoma a cikin karamin farashi wanda wannan shakka babu zai tayar da komadar tattalin arzikin wannan kasa, in Allah ya kai mu malko nagaba zamu dora.

Subscribe to:
Posts (Atom)