Noman rani ko noman ban ruwa kamar yadda muka sani shine zuba ko sanya ruwa a gona ko kuma wata hanya ta gudanar da aikin gona ba tare da dogaro da ruwan sama ba ko zuwan damina ba kamar a wasu wuraren da suke da karancin ruwan sama ko ake samun yankewar ruwan sama a tsakiyar damina. Bayan wannan noman ban ruwa yana taimakawa wajen kara girman amfanin gona, kula da filin noma,sake rayar da filin noma musamman a lokacin rani.Amfanin noman ban ruwa ga amfanin gona ko da ita gonar kanta bai tsaya anan ba domin yana taimakawa wajen kare amfanin gona daga kwari,kassara ciyayin da suke fitowa a cikin gona, yana taimakawa gaya wajen hana zaizayar kasa a cikin gona, sannan yana ba da damar yin shuka fiye da sau daya a shekara.
TAKAITACCEN TARIHI
Noman ban ruwa kamar yadda dalilai na tarihi da binciken masana suka tabbatar abune mai dadadden tarihi musamman yankunan hamada da kuma yankunan da suke gabar koguna.Bincike ya tabbatar da shekaru masu yawa kafin haihuwar Annabi Isa ake noman ban ruwa a kogin nan na FURATA (AL-FURAT) dake aksar Iraki. A nahiyar afirika ma noman ban ruwa an fara shine a wajen karni na farko zuwa karni na biyu kafin haihuwar Annabi Isa wanda ya dogara ne da jan ruwa daga koguna kamar kogin nan na Nilu da sauransu.Amma samun cigaba na zamani da kuma shigowa injina masu aiki da man gas ko wutar lantarki wannan ya bunkasa harkar noman ban ruwa matuka gaya ta inda irin wadannan injinan tso-tso ruwa (pumping machine) sukan iya tso-tso miliyoyin lita na ruwa cikin takaitaccen lokaci.
Mizanin amfani da kayayyakin noman ban ruwa a duniya ya kai wajen kilomita 2,788,000 (wato eka miliyan 689) ta gonaki noma masu dauke da injinan ban ruwa a shekarar 2000. Inda wajen kashi 68 cikin dari na wadannan gonaki suna yankin ashiya ne inda kashi 17 yake ya ke a kasar Amurka,kashi 9 a nahiyar Turai yayin da kashi 5 cikin dari yake nahiyar mu ta Afirika.Inda aka fi noman ban ruwa a duk faduin duniya shine arewacin indiya da fakistan kusa da kogunan da ake kira da GANGES da INDUS. Binciken baya-bayannan da aka gudanar a shekarar 2008 ya nuna ana amfani da wajen kilomita 3,245,566 wanda ya kai kusan fadin kasar Indiya gaba dayanta.
Wadansu kamar yadda muka fada suna amfani da injina don ban ruwa a gona yayin da wasu kuma suke amfani da bokitai da butoci dan yi ban ruwa a gona da sauran hanyoyi masu yawa wanda in mun samu dama nan gaba zamu kara fadada bayani gamsashshe akai.Amma ya kamata mu sani cewa mu mun saba muna kiran irin wannan noma da noman rani a kasashe irin su Iran yawancin noman da a keyi ana yinsa ta hanyar ban ruwa a gona ko da kuwa a lokutan damina ne saboda karancin ruwan sama da suke fama da shi.Wani bincike da hukumar noma da abinci ta majalisar dinkin duniya ta wallafa a shekarar 1991 ya nuna a yankin Afirika ana amfani da kadada milyan 6 ne kawai wajen noman ban ruwa a cikin kadada miliyanm 40 da za'a iya wannan aiki dasu.Duk da haka zami kira ga gwamnatocimu kan su taimakawa manomanmu da injinan zamani na ban ruwa don kara yawan abincin da ake samarwa a wannan kasa.Sai mun hadu a mako na gaba. NAGODE.
No comments:
Post a Comment