Sunday, 13 May 2012

KAYAYYAKIN AMFANI A CIKIN GONA (FARM INPUT) 2

TAKI
Barkan mu da sake saduwa a wannan mako, waccan makon mun tattauna akan iri da nau'o'insa wannan mako in Allah ya yarda zamu yi bayani ne akan takwararsa wato Taki.Taki kamar yadda muka sani shine abinda shuka take sarrafawa ta mai dashi abinci.Binciken masana kimiyyar gona ya tabbatar da muhimmanci da gudummawar da taki yake badawa wajen bunkasa yabanya da kuma kariyar da yake bawa kasar gona daga lalacewa in anyi amfani dashi yadda ya kamata.Sai dai har yanzu akwai matsaloli nan da can wajen samar da taki mai inganci da kuma karancin ilimi ga manoma kan yadda zasu yi aiki dashi acikin gona.
GABATARWA
Binciken kimiyyar aikin gona ya tabbatar cewar kasa tana kunsheda  sinadarai masu yawa wanda kwari suke sarrafawa domin samar wa kansu abinci.Wadatar wadannan sinadarai a kasa shine yake alamta karfin da kasa take dashi,wato dacewarta da rayuwar kwari da shuke-shuke. A sanadiyar noma kasa da ake da girbi har na tsawon wani lokaci wannan ya danganta da yanayin kasar wajen  domin wata tafi wata karfi  saboda sinadaran da suke kunshe a cikinta, ana nomata karfinta yana raguwa ahankali-ahankali ana gane haka ne kamar ta hanyar raguwar yawan amfanin gona da aka saba girba a kanta. To idan kasa ta kasance a irin wannan yanayi na rashin karfi,zaka ga su kansu kwari sun kasa samun isashshen abinci da suke bukata ballanrtana har su sarrafashi ya zama yabanya tai kyau. A irin wannan yanayi ne ake amfani da taki kona gargajiyya kona zamani domin dawowa da wannan kasa karfi da danko.
MENE NE TAKI
Taki shine wadansu sinadarai  masu rai ne  ko  mara sa rai da ake sarrafawa, wanda ake zubawa akan kasa don a samu karin kuzari ga kasa ta yadda ita kuma yabanya zata bunkasa.Binciken da muka gabatar kwanan nan ya nuna wajen kashi 40-60 cikin dari na yawan abincin da ake nomawa ya ta'allaka ne kacokan kan amfani da taki a gona, domin karfin taimakon da yake bawa yabanya ta fuskar saurin girma da girbar amfani mai yawa.Hakanan binciken ya tabbatar da kasuwar taki a duniya zata kai sama da naira tiriliyan 3 daga nan zuwa shekarar 2018. Harsashe ya nuna wajen fiye da rabin mutanen duniya suna samun abincin da zasu cine ta hanyar wannan fasaha ta amfani da taki a gona.
YANAYI
Taki yana zuwa a nau'o'i da dama sananne shine ya zo a daskare kamar gari sannan yana zuwa a nau'in ruwa wanda yafi kowane nau'i cikin nau'i kan taki saurin game gona.
IRE-IREN TAKI
Akwai takin da ake sarrafawa ta hanyar ma'adanai wato takin da ake sarrafawa daga abubuwa marasa rai kamar sainadarin kanwa (potasium).Akwai kuma takin da ake sarrafawa daga abubuwa masu rai kamar su dabbobi da kwarika, da kuma abin da yak fitowa daga garesu kamar kashin su, da dai sauran abubuwa masu saurin rubewa. irin wannan taki shi ake kira da takin gargajiyya.
Takin zamani shi ya hada dangogi biyun, wato na ma'adanai da wanda ba na ma'adanai, wanda yawanci shi takin zamani ana sarrafa shine a masana'antu domin sayarwa ga manoma.
A karshe yawa da nau'in takin da ya kamata ai amfani dashi a gona ya dogara ne ga yanayin kasa da kuma nau'in amfanin da za'a shuka a wannan kasa. Malaman gona su kan yi gwaje-gwajen kasa ko yanki domin gane dangin taki da kuma yawan da kowane yanki ke bukata wannan dalilin ne yasa muke nanata kira ga manoma dasu dinga neman shawarwarin malaman gona kafin su kai ga zuba taki a gonakinsu. Wanda muma in Allah ya yarda duk amfanin gonar da  muke bayani akansa zamu fadi nau'i da yawan takin da yake bukata in Allah ya yarda. Mako na gaba zamu dora




















No comments:

Post a Comment