A wannan makon da yardar mai duka zamu tattauna ne kan abin da ya shafi wajibai a cikin harkar noma wadanda inka cire gona ba wani abi da ya kai su muhimmanci a wannan sana'a ta noma. wadannan abubuwa da suka hada da Iri,Taki,Magunguna da kuma kayayyakin aiki na gargajiyya kamar su fatanya,magirbi da sauransu da kuma na zamani irin su motar tirakta da sauransu.Wadannan kayayyaki in anyi amfani dasu yadda ya kamata to shakka babu za'a samu amfani mai yawa kuma lafiyayye.
IRI
Iri shine dukkan wata kwaya ko tushe da aka shuka a kasa don a samu abinci ko amfani. Kaga kenan iri yana da matukar muhimmanci a harkar noma fiye da sauran yan'uwansa irin su taki da magani domin shi in ba 'a sa iri ba to ba maganar a girbi amfanin gona.Daga nan zamu fahimci cewa matukar ana so a samu wadataccen abinci da kayan sarrafawa a masana'antun mu da suka dogara da amfani gona wato (agro-allied industries) to abi na farko da za ai shine samar da ingantaccen iri kuma a wadace cikin saukin farashi.
Ana samun ingantaccen iri ta hanyoyi kamar haka a wannan zamani; ana samun ingantaccen iri mai nagarta da inganci ta hanyar binciken ilimin kimiyya wanda yawanci malaman kimiyyar aikin gona ne suke aiwatar da shi ta hanyar bin diddigi da dogon nazari da bincike na tsawan lokaci har su kai ga fitar ko samar da ingantaccen iri mai juriya kuma mai yalwa.Bayan wannan hanya manoma ma suna da wata dabara ko fasaha wajen fitar da ingantaccen iri shine sukan dau iri kaza na amfani kaza su gwada, a haka har su fitar da me kyau lafiyayye sa'annan su fitar da baragurbi.
Lallai indai ana so a samar da abinci mai yawa da inganci a wannan yanki namu da ma kasa baki daya to dole ne a samar wa manoman mu fasahar noma ta zamani a kuma dinga wayar musu da kai akan sababbin hanyoyin noma na zamani ta hanyar ilimintar dasu da basu shawarwari nagari. Hakanan dole a samar musu da irin noma na zamani kamar irin masara,tumatir,gero,alkama,rogo da sauransu wato nau'in abincin da mutanen yankin suka saba dashi.Cibiyar nan ta international institute of tropical agriculture (IITA) dake da mazauni a garin ibadan ta dade tana fitar da iri na zamani ga manoma. misali wani sabon iri da ta fitar na shinkafa na zamani wanda da in ka shuka irin da muka saba dashi a kadada 1 zaka girbi abin da baifi tan 2 ba na amfanin gona,amma wannan sabon iri inka shuka shi a kadada 1 zaka gibi amfanin gona da yakai tan 3-6 .Sannan ire-iren irin da ake shigowa dasu daga kasashen ketare kamar wani irin tumatir da aka shigo dashi daga kasar demmak zuwa najeriyya wanda manoman da suka gwada shi sun tabbatar da ingancin sa ta hanyar saurin nunarsa ga tsoka ga yalwa ga juriya da kuma girma.
A karshe mun gane muhimmancin iri a harkar noma tokuwa in hakane ya zama wajibi muyi kira ga gwamnatoci da su shigo cikin wannan harka ta samar wa manoma iri ingantacce domin ko a kasashen da suka cigaba irin wannan aiki sai manyan kamfanoni masu zaman kansu ne suke iya daukar dawainiyyar wannan aiki saboda daukar lokaci da kuma tsada.Kaga kenan in gwamnati ta shigo ciki zata tabbatar da fitar da wadataccen kudi da za'ai wannan aiki dasu,sannan tayi maganin matsalolin da manoma suke fuskanta inda suke asara yayin da suka sayi iri ba mai nagarta ba, kasancewar yawancin manoman wannan yanki namu masu karamin karfi ne to shigowar gwamnati ciki zai tabbatar da samar da iri mai inganci ga manoma a cikin karamin farashi wanda wannan shakka babu zai tayar da komadar tattalin arzikin wannan kasa, in Allah ya kai mu malko nagaba zamu dora.
No comments:
Post a Comment