NOMAN WAKEN-SUYA (5)
Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo domin kara wayarwa da manoman mu da masu sha'awar shiga wannan harka ta noma da kiwo tare da yin tsokaci kan alfanun dake ciki, musamman ma a kokarin da muke domin bunkasa tattalin arzikin wannan kasa. Kamar yadda muka dau akalla fiye da wata guda muna tattauna abin da ya shafi noman waken-suya a yau da yardar mai-duka zamu dora daga inda muka tsaya a makon daya gabata.
WAKEN-SUYA: TAKI
Adadin yawan takin da gona ke bukata domin noman waken-suya ya ta'allaka da irin dandanan kasar da kuma yankin da gonar take. Kamar yadda mu kai tsokaci a baya kuma akasarin manoman waken-suya suka sani cewar waken-suya baya bukatar takin dake kunshe da sinadarin NITROGEN kasancewar da kansa yake samarwa kansa wannan sinadari, kuma kamar yadda binciken masana kimiyyar noma ya nuna waken-suya na dogara ne kacokan da sinadarin NITROGEN domin girma. Binciken kuma ya tabbatar da karancin sinadarin PHOSPHURUS a waken-suya don haka ake bukatar manomi da ya zuba taki mai dauke da wannan sinadari na PHOSPHURUS domin samun amfani mai yado. Ana bukatar manomi ya zuba sinadarin PHOSPHUROS da yakai adadin kilo 30 a duk kadada guda (hecter) ta hanyar amfani da takin da ake kira da (super phosphate fertiliser). Hakanan taki mai dauke da sinadarin NITROGEN da POTASSIUM ana zuba sune kawai a yayin da manomi ya fahimci karancin su kuru-kuru a cikin gona. A kan iya cakuda takin da ake son amfani dashi yayin yin sharar gona ko lokacin yin haro (Harrow).
NOMAN WAKEN-SUYA: TAGOMASHI
Kamar yadda muka fada a baya waken-suya na kara tagomashin gona ta hanyar sanya adadi mai yawa da gona ke bukata na sinadarin NITROGEN a cikin kasa. Musamman ma idan manomi ya shuka shi tare da masara (wadda in Allah ya yarda zamu tattauna akan noman ta nan gaba kadan) yana taimakawa gaya wajen kashe muguwar ciyawar nan da ake kira da stringa hermonthinca.
KWARIRRIKA DA CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA HANYOYIN MAGANCE SU A GONA.
CIYAYI DA YADDA ZA'A MAGANCESU
Ciyayin dake addabar waken-suya duk shekara ko kuma a shekara sau biyu , wato lokacin noman damina da kuma lokacin noman rani , sun fi addabar waken-suya yayin da yai tsiro ya dan fara girma. Don haka tashi tsaye ga manomi akan lokaci domin magance wannan matsala kan iya rage karfi da kuma tasirinta a jikin waken-suya. Manomi kan iya magance tasirin ciyayi a cikin gona ta yin amfani da hanyoyi guda biyu da zamu ambata, wato ko dai ta yin amfani da hanyar gargajiyya ko kuma ta yin amfani da hanyar zamani.
HANYAR GARGAJIYYA; anan ana bukatar manomi ya fara nome ciyayin da suka fito a cikin gona sati biyu bayan shuka, sannan sai ya bari sai bayan sati na biyar zuwa shida da yin shuka ya kara yin wata nomar. Yana da kyau manomi ya kiyaye yin gaggawa wajen yin noman ciyayin gona tun kafin ruwan sama ya kan-kama domin yin hakan zai iya zama yin aikin baban giwa. Hakanan yin noman ciyawa mara kyau ko kuma dogon jinkiri wajen nome ciyayi zai iya rage yawan amfanin da za'a samu in girbe waken-suya.
HANYAR ZAMANI; anan ana bukatar manomi yai amfani da magungunan feshi don kashe ciyayin da suka fito yayin noman waken-suya. Magungunan feshin ciyayi suna da tasiri sosai in manomi yayi amfani dasu yadda ya kamata. Kazalika zaben magani kashe kwari daya kamata manomi yai amfani dashi a cikin gonar sa ya ta'allaka da iri yanayi ciyawar da ta fito da kuma saukin samun maganin a inda manomin yake. Duk da cewa magungunan kashe ciyayi suna nan a wadace ga ciyayin da basu bayyana ba dama wadanda suka bayyana a cikin gona. Don haka in aka fesa maganin kashe ciyayi a cikin gona, manomi zai fara nome ciyawa da zarar an shiga sati na biyar zuwa shida da shuka waken-suya a cikin gona.
Da yardar Allah mai kowa mai komai zamu kammala wannan mukala a mako mai zuwa. NAGODE.
Allah ya saka da alkhairi Dan Allah ko za'a bamu bayani game da noman ridi ?
ReplyDelete