Monday, 25 November 2013

TURAKU GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (2)

                                                         TURAKU GOMA SHA DAYA NA
                                                            CIN NASARA A HARKAR
                                                                NOMA DA KIWO (2)



(6) Yaya kana da dagiya kan al'amura? gudanar da harkar noma na da wahalar gaske, wanda wannan zai iya janyo wa mutum gazawa a wadansu lokutan. Saboda yawancin  mamallakan wannan harka sukan gaza wajen daukar nasara ko rashinta.  Don haka kana bukatar ka dunga samun karfafa gwuiwa a kowanne lokaci don cigaba da dorewar  wannan harka, da kuma kariya daga gurguncewar harkar da makamantansu. Domin kuwa da wannan harka tana da sauki gaya da kaga kowa   a cikin ta.  Anan ya kamata mu ari karin maganar nan da take cewa  idan kana son kayi sukuwar sallah a wannan harka ta noma da kiwo, dole ka zamto ka shirya faduwa daga kan dokin ka sau shurin masaki ba tare daka sare ba.


(7) Yaya harkar noma zai shafi iyalanka? Babu tantama cewar a farkon lokacin daka fara wannan harka  zai dan shafe ka da yarda kake gudanar da harkokin iyalanka ta bangaren  kudi.  Wannan kuwa  kan iya daukar watanni kai har shekaru ma kafin akai ga fara cin riba. Don haka wajibi ka shirya yadda zaka dan gyatta yadda kake gudanar da wadannan harkoki damin samun alheri mai yawa nan gaba kadan.


(8) Shin ka dau wadataccen lokaci kana nazari kan wannan harka don ganin ko akwai alheri a ciki kuwa? Kai sani zaka shiga harkar noma da kiwo ne da nufin samun alheri. Don haka kada kai gaggawa ba  tare daka shirya fuskantar kalubalen dake tattare  da wannan harka ba. Yana da kyau ka halarci tarurruka na karawa juna sani, sayen littafai na harkokin noma da kiwa da jaridu, mujallu da kuma mudawwanoni na wannan harka kamar dandalinnomadakiwo.blogspot.com.


(9) Shin kana da gogewa  kan irin harkar da zaka gudanar?  Yawancin wadanda suka cigaba sukai kaurin suna a wannan harka sun kasance suna da gogewa a wannan harka tun kafin sukai ga shiga cikinta ka'in da na'in. Ka halarci lakcoci kan wannan harka tun kan ka kai da fara wannan harka.


(10) Shin kana da karfin jari?  Rashin kudi   yawanci shine kashin bayan karya ko  gurgunta yawancin harkokin kasuwanci bawai kawai noma da  kiwo ba. Don haka kana  bukatar jari wadatacce domin gudanar da wannan harka yadda ya kamata.



(11) Shin kana iya sayarwa?  Kowanne  iri harkar kasuwanci na bukatar abokan hulda wato (customers) , wanda ake bukatar ka ka fara tuntuba tun farkon lokacin fara gudanar da wannan harka.  Yana da kyau kayi kokari kan bunkasa bangaren daya shafi saye da kasuwanci na wannan harka domin kuwa in dai hajarka bata karbu ba to kuwa wannan ya zama abin da ake kira anyi ba ai ba.



Da wadannan muhimman tambayoyi guda goma sha daya muke ganin duk wanda ya samu damar amsasu yadda ya kamata, zai shiga wannan  harka ta fatan samun nasara gwaggwaba na bada dadewa ba. Allah ya sanya albarka ya taimake mu akan dukkanin al'amuran mu na alkhairi kuma ya datar damu akan yin daidai. Da yardar mai-duka mako mai zuwa zamu tattauna abin da ya shafi kiwo.  NAGODE


Monday, 18 November 2013

TURAKUN GOMA SHA DAYA NA CIN NASARA A HARKAR NOMA DA KIWO (1)

                                          TARAKU GOMA SHA DAYA NA CIN
                                               NASARA A HARKAR NOMA
                                                        DA  KIWO (1)


Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mako a wannan dandali namu  mai albarka na dandalin noma da kiwo inda mukan tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo tare da yin tsokaci kan wadansu muhimman bayanai na masana da nufin yin wukar gindi dasu domin fadakar da al'umarmu na birni da karkara kan yadda zamu cicciba wannan muhimmiyyar sana'a tamu ta noma da kiwo da muka gada tun iyaye da kakanni. Allah kadai muke roko ya karba mana kuma ya inganta mana kasar nomanmu da kiwo domin cigaban tattalin arzikin wannan kasa tamu  mai tarin albarka. A yau da yardar mai-duka zamu tattauna ne akan wadansu turaku ko dabaru muhimmai kan yadda masu wannan harka ta noma  da kiwo zasu kai ga bunkasa sana'arsu.

A kasance tare damu.



GABATARWA.



Yana da  kyau ga duk mai  niyyar shiga wannan harka ta noma da kiwo ya kwan da sanin cewa akwai hadurra dake cikin wannan harka wanda hakan ke nuna cewa samun nasara a cikin ya ta'allaka kacokan ga sa'a da kuma bin abubuwa sau da kafa.  Samun  nasara a wannan harka ta noma da kiwo ya dogara da irin hangen nesa da kuma kyakkyawan tsari wajen gudanar da wannan harka mai tsananin riba.  Fara wannan harka ta noma da kiwo zai bawa  mutum damar  da yake bukata ta zama mai dogaro da kansa, amma kafin ka kai ga farawa  ya kamata ka fara bincikar kanka  ta hanyar da zaka gane inda kake da karfi da kuma inda kake da rauni wajen gudanar da wannan harka ta noma da kiwo. Ayin hakan yana da kyau ka tambayi kanka  wadannan muhimman tambayoyi wanda bada amsarsu zai taimaka maka gaya wajen shiga wannan harka ko dakatar da shiga zuwa wani lokaci nan gaba.


(1) Shin kai farin shiga ne?


Kasancewar ka sabo a wannan harka yana da kyau ka zama ka samu dukkan karfi da zuciya da zaka iya jurewa wannan aiki, da kuma daukar muhimman tsarirrika da zasu taimakawa  cigaban wannan harka ta noma da kiwo.  Harkar noma da kiwo na bukatar kwazo da aiki tukuru, yana bukatar kokari da juriya da zai baka damar yin aiki mai yawa a kowacce rana wanda ba zasu yiwu ba har sai ka tursasawa kanka yinsu.


(2) Yaya mu'amalarka take da sauran mutane?

A matsayinka na manomi nasararka tana da alaka da yadda dangantakar ka ta kasance da sauran mutane, wadanda suka hada da sauran yan'uwa manoma, abokan ciniki, cibiyoyin bincike kan harkar data shafi noma da kiwo,dillalai,bankuna, lawyoyi, masana harkar shige da ficen kudi, mutanen garinku, da kuma sauran al'umma. Yana da kyau ka tabbatar ka fitar da nagartattun hanyoyi da zasu taimaka wajen biyan bukatun abokan cinikinka.


(3) Shin ka iya daukar matakai masu kyau?

Ana gane shugaba ne ta hanyar daukar matakai masu kyau, don haka ana bukatar manoma su dunga daukar matakai akan lokaci, cikin gaggawa, domin tabbatar da samun nasara a wannan harka ta noma da kiwo.


(4) Shin kana da karfi na zahiri da karfin zuciya na iya gudanar da wannan harka?


Gudanar da harkar noma da kiwo na bukatar mai da hankali kacokan ga mai gudanar da wannan harka. Babu batun buya ko labewa ga mai yin wannan harka a matsayin ta na yar lelenka. Ko uwa tana guduwa wajen shayar da yarta ne? Kasancewar ka a wannan harka yana da dadi duk da cewa akwai ayyuka masu yawa da kalubalai. Dole ka tsara lokutan ayyukan ka , amma a lura duk abin daya kamata ayi a tabbatar anyi shi akan lokaci cikin gaggawa.


(5) Shin kana da tsari mai kyau da iya gudanarwa?


Kamar yadda muka sani cewar rashin tsari shine babban abin da yake rugurguza yawancin harkoki ba ma kawai na noma da kiwo ba. Kai sani cewa tsarin gudanar da harka mai kyau yana taimakawa wajen kaucewa hadurra masu yawa.


Anan zamu dakata da yardar Allah zamu dora a mako na gaba.  NAGODE.

Monday, 4 November 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (6)

NOMAN WAKEN-SUYA  (6)



Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da  suka  shafi noma da kiwo wani zubin kuma muyi tsokaci kan wani cigaba ko wata ribar kafa da aka samu duka fatanmu shine bunkasa tattalin arzikin wannan kasa tamu wadda Allah madaukakin sarki ya albarkaceta  da  dukkan abin da dan adam ke bukata a rayuwarsa. Idan mai karatu bai manta a makon daya gabata  a cikin wannan mukala tamu mai albarka ta noman waken-suya muna tattauna abin daya shafi yadda za'a magance ciyayi da ka iya addabar  waken-suya  a cikin gona. Da yardar mai-duka a wannan mako zamu kammala wannan mukala. Ku biyo mu.


KWARIRRIKA DA YADDA ZA'A MAGANCESU A GONA YAYIN NOMAN WAKEN-SUYA.

Akwai kwarirrika nau'i daban-daban a cikin gona yayin da ake noman waken-suya, amma binciken masana ya tabbatar da cewa kadan ne cikin wadannan kwarukan masu amfani   ga waken-suya. Kuma masanan sun tabbatar da cewa jinsunan kwarirrika masu cutar da waken-suya a wannan kasa kadan ne,wanda ba zai bada wata babbar wahala ba wajen magancesu.  Babbar hanyar magance barnar kwari  a cikin gonar waken-suya shine ta hanyar amfani damaganin feshin kwarin  nan na CYPERMETHRIN+DIMETHOATE da ya kai alkaluma 100 na ma'aunin (ML) a cikin adadin litar ruwa 15.


CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA YADDA ZA'A MAGANCE SU.

Cututtukan dake addabar waken-suya a wannan kasa su kan yi tasiri sosai wajen hana shi yin yado. Hanyoyin da manomi zai bi kuwa domin magancesu sun hadar  da;

-shuka irin waken-suya mai juriya: wannan itace dabara mafi dacewa awajen maganin cututtukan dake addabar waken-suya.

-Yin gyara da sharar gona mai kyawu: kuma manomi ya kiyayi shuka waken-suya akan busasshiyar kasa.

-Shuka irin da aka tufatar dashi da maganin kasahe kwari da cututtuka: kamar yadda mukai bayani a baya.

-Noman hadaka da sauyi wajen noma waken suya da masara: yin hakan na karawa gona tagomashin daya kamata wajen yaki da cututtuka.

-Ta hanyar  yin amfani  da magungunan  yaki da  cututtukan dake  addabar waken-suya a cikin gona.



             GIRBE WAKEN-SUYA


Yawanci kamar yadda muka sani waken suya na isa girbi yayin da yakai wata 3 zuwa 4 da shukawa. Bayan  haka waken-suya  na bukatar gaggawa ta musamman wajen girbi, domin kuwa  kin yin hakan zai iya kawo asara mai  yawa.  Saboda  haka ana so a girbe  waken-suya da anga  kaso 85 cikin 100 ya  koma kalar ruwan kasa. Akan iya girbe waken-suya ta hanyar amfani da  adda,fartanya ko kuma lauje.  Manomi ya  tabbatar ya yanko shukar waken-suya tun daga tushiya.  Daga nan ana bukatar manomi ya shanya waken-suya daya  girbe akan tamfol har zuwa tsawon akalla makonni biyu. Yana da kyau manomi ya guji  yin amfani da hannu wajen girbe waken-suya, domin yin hakan zai iya fitar da sinadaran da waken-suya ya zuba a cikin gona.  Daga bayan manomi ya tabbatar da cewar waken-suyan sa ya bushe yadda ya kamata sai BUGU.  Bugu shine kamar yadda muka sani zuba waken-suya dake cikin konsonsa a cikin buhu sai a dinga duka da icce.


             AJIYAR WAKEN-SUYA


Waken-suya ya bushe yadda ya kamata idan aka kasa gatsa shi  da hakoro ko kuma da dan-yatsu. A zuba kilo 50 ko kuma kilo 100 na waken-suya a cikin buhu mai kyau a rufe a cikin rufaffen rumbu ko kuma kasan inuwa. Manomi ya lura cewa  yiwa waken-suya kyakkyawar  ajiya zai  taimaka masa gaya wajen samun kariya daga kowanne irin lahani ko tawaya da kuma yin  saurin tsiro  yayin da akai niyyar yin  amfani dashi  a matsayin iri a cikin gona.


          KAMMALAWA


A karshe muna sanar da masu karatun mu cewa wannan mukala kan yadda za'a shuka waken suya ta tsaya daga nan, muna  bukatar  ra'ayoyinku akan abubuwan da muka tattauna, kuma in Allah ya bamu yawan  rai zamu tattauna yadda ake sarrafa da kasuwancin waken-suya. NAGODE.

Monday, 28 October 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (5)

   NOMAN WAKEN-SUYA (5)

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai farin jini na noma da kiwo inda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo domin kara wayarwa da manoman mu da masu sha'awar shiga wannan  harka ta noma da  kiwo tare  da  yin tsokaci kan alfanun dake ciki, musamman ma  a  kokarin da muke domin bunkasa tattalin  arzikin wannan kasa. Kamar yadda muka dau akalla fiye da wata guda muna tattauna abin  da ya shafi noman waken-suya a yau da yardar mai-duka zamu dora daga inda muka tsaya a makon daya gabata.


WAKEN-SUYA: TAKI


Adadin yawan takin  da gona ke bukata domin noman waken-suya ya ta'allaka da irin dandanan kasar da kuma yankin da gonar take.  Kamar yadda mu kai tsokaci a baya kuma akasarin manoman waken-suya suka sani cewar waken-suya baya bukatar takin dake kunshe da sinadarin NITROGEN kasancewar da kansa yake samarwa kansa wannan sinadari, kuma kamar yadda binciken masana kimiyyar noma ya nuna waken-suya na  dogara ne  kacokan  da sinadarin NITROGEN domin girma. Binciken kuma ya tabbatar da karancin sinadarin PHOSPHURUS a waken-suya  don haka ake bukatar manomi da ya zuba taki mai dauke da wannan sinadari na PHOSPHURUS domin samun amfani mai yado.  Ana bukatar manomi ya zuba  sinadarin PHOSPHUROS da yakai adadin kilo 30  a duk kadada guda (hecter)  ta hanyar amfani da takin da ake kira da  (super phosphate fertiliser).  Hakanan taki mai dauke da sinadarin NITROGEN da POTASSIUM  ana zuba sune kawai a yayin da manomi ya fahimci  karancin su kuru-kuru a cikin gona.  A kan iya cakuda  takin  da ake son amfani  dashi  yayin yin  sharar gona ko  lokacin yin haro (Harrow).


 NOMAN WAKEN-SUYA: TAGOMASHI


Kamar yadda  muka fada  a baya waken-suya  na kara tagomashin  gona ta hanyar sanya adadi mai yawa da  gona ke bukata na sinadarin  NITROGEN a cikin kasa.  Musamman ma idan manomi ya shuka shi tare da masara (wadda in Allah ya yarda zamu tattauna akan noman ta nan gaba kadan) yana taimakawa gaya wajen kashe muguwar  ciyawar nan da ake kira da   stringa hermonthinca.

KWARIRRIKA DA CUTUTTUKAN DAKE ADDABAR WAKEN-SUYA DA HANYOYIN MAGANCE SU A GONA.


CIYAYI DA YADDA ZA'A MAGANCESU

Ciyayin dake addabar waken-suya duk shekara ko kuma a shekara sau biyu , wato lokacin noman damina da kuma lokacin noman rani , sun fi addabar waken-suya yayin da yai tsiro ya dan fara girma. Don haka tashi tsaye ga manomi akan lokaci domin magance wannan matsala kan iya rage karfi da kuma tasirinta a jikin waken-suya. Manomi kan iya magance tasirin ciyayi a  cikin gona ta yin amfani da hanyoyi guda biyu da zamu ambata, wato ko dai ta yin amfani da  hanyar gargajiyya ko kuma ta yin amfani da hanyar zamani.


HANYAR GARGAJIYYA; anan ana bukatar manomi ya fara nome ciyayin da suka fito a  cikin gona sati biyu bayan shuka, sannan sai ya bari sai bayan sati na biyar zuwa shida da yin shuka ya kara yin wata nomar. Yana da kyau manomi ya kiyaye  yin gaggawa wajen yin noman ciyayin gona tun kafin ruwan sama ya kan-kama domin yin hakan zai iya zama yin aikin baban giwa. Hakanan yin noman ciyawa mara kyau ko kuma dogon jinkiri wajen nome ciyayi zai iya rage yawan amfanin da za'a samu in girbe waken-suya.


HANYAR ZAMANI; anan ana bukatar manomi yai amfani da  magungunan feshi don kashe ciyayin da suka fito yayin noman waken-suya. Magungunan  feshin  ciyayi suna da tasiri sosai in manomi yayi  amfani dasu yadda ya kamata.  Kazalika zaben magani kashe kwari daya  kamata manomi yai amfani dashi  a cikin gonar sa ya ta'allaka da iri yanayi ciyawar da ta fito da kuma saukin samun maganin a inda manomin yake.  Duk da cewa magungunan kashe ciyayi suna nan a wadace ga ciyayin da basu bayyana ba dama wadanda suka bayyana   a cikin gona.  Don haka in aka fesa maganin kashe ciyayi  a cikin gona,  manomi zai fara nome ciyawa da zarar an shiga sati na biyar zuwa shida da shuka waken-suya a cikin gona.

Da yardar Allah mai kowa mai komai zamu kammala wannan mukala a mako mai zuwa.  NAGODE.

Monday, 21 October 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (4)

NOMAN WAKEN-SUYA  (4)


Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka na noma da kiwo inda muke tatttauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo musamman a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa domin ganin mun ba da gudummawa wajen cicciba tattalin arzikin wannan yanki namu da kuma kasar mu baki daya.

wannan dandali na taya ku  murnar barka da babbar sallah da fatan Allah ta'ala ya karbi ibadun mu da yankanmu. Wannan dandali kuma yana mai addu'a ga  alhazan mu  da suke can kasa mai tsarki (Makka) domin gudanar da ibadar aikin hajji Allah ta'ala ya karbi ibadunsu kuma  ya dawo  mana su gida lafiya.  Amin


GWADA KARFIN IRIN WAKEN-SUYA

Yana da kyau manomi ya tabbatar kafin ya kai ga shuka irin waken-suya ya tabbatar ya jarraba irin domin ta hanyar hakane zai iya gane ko irin da zai amfani dashi mai kyau ne kuma mara kyau ne. Idan ya samu kashi 85 cikin dari (85%) na irin da ya shuka sun yi tsiro to mai kyau ne, manomi zai iya shuka wannan irin. 

Yadda manomi zai iya ganewa cewa irin sa mai kyau ne kuwa shine ya debi iri akalla guda 400 sai ya kasa su gida hudu ya shuka a wajen daya tanada domin gwajin iri, inda zai  kasa wurin  zuwa gida hudu ya shuka kowanne iri 100 a waje daban. Zai shuka kowanne iri ta hanyar ba da tazarar santimita (centimetre) 10 a tsakani. Ya tabbatar yana zuba isasshen ruwa safiya da maraice (yammaci).  Manomi kan  iya fara kirga irin da yai tsiro daga kwana biyar zuwa kwana goma, daga nan  inya samu tsiro 320 ko sama da haka (wanda ya kai kashi 80 cikin 100 (80%) kenan ka sama da haka) zai iya shuka wannan irin tare da kyakkyawar fatan samu amfani mai yawa.

             SHUKA WAKEN-SUYA

LOKACIN SHUKA

A kan iya shuka waken-suya a lokaci daban-daban, domin kuwa wannan ya ta'allaka da yanayin wajen da manomi yake kamar yadda  zami bayani nan  gaba kadan da yardar mai-duka. Dan haka ba'a son manomi ya shuka waken-suya da wur-wuri tun gabanin ruwan sama ya kan-kama don yin hakan zai iya zama aikin baban giwa inda zai zame wa manomi aiki biyu don kuwa sai ya sake shuka   wani irin.  Kazalika ba'a son yin jinkiri wajen shuka waken-suya, domin jinkirin zai iya kawo kwari da sauran munanan cututtuka da zasu iya  ragewa amfani karsashe. Saboda haka ana bukatar manomi ya shuka irin waken-suya daga  lokacin da ruwan sama ya kan-kama.


ADADIN IRIN WAKEN-SUYA DA AKE BUKATA

Idan manomi ya shuka kilo 50 zuwa 70 na irin waken-suya akwai kyakkyawar yiwuwar samun tsirrai dubu dari hudu da dari hudu da arba'in da hudu wato (444,444) a kowacce kadada guda. Amma tun da irin waken-suya ya banbanta daga girma  zuwa girma (inda  zaka samu iri na waken-suya guda 100 ya kai nauyin giram 12.6 wani kuma ya kan kai giram 18.9).

TUFATAR DA IRI
Yana da kyau ga kowanne manomin waken-suya ya tabbatar  kafin ya kai ga shuka irin sa ya tufatar dashi da magungunan cututtuka da kuma kwari. Manomi kan iya amfani da sanannen maganin nan na APRON PLUS ko THIAM. Duk jaka daya wato (sachet) a cakuda shi a cikin iri  daya kai kilo takwas kafin shuka domin samun kariya daga cututtukan dake  addabar waken-suya a cikin  gona.

YADDA AKE SHUKA WAKEN-SUYA DA KUMA TAZARAR DA YAKAMATA MANOMA SU BARI.

Manomi kan iya shuka ta hanyar yin  amfani  da hannu  ko kuma abin shuka. Manomi ya  shuka waken-suya  guda uku zuwa hudu  a kowanne rami, kana ya  bada tazarar santimita (Centimetre)  75 a kwance da kuma santimita 10 a tsaye.  Amma  ga irin waken-suya mara dogon-zango manomi kan  iya  shuka  shi ta  hanyar barin tazarar santimita  50 a kwance da kuma santimita 5 a tsaye, saboda kasancewar iri  waken-suya mara dogon-zango sun fi jin dadin tazara mai kunci ba kamar irin waken-suya  mai  dogon-zango ba.  Manomin waken-suya ya tabbatar ya kula sosai wajen ramin da zai zuba irin waken-suya kada zurfin ya kai santimita biyu zuwa biyar.  Domin kuwa yin ramin da za'a zuba waken-suya  da zurfi ya kan iya hanashi yin  tsiro kwata-kwata.


LOKACIN DA AKA FI SON A SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.

Lokaci abin so bisa ga binciken masana don shuka waken-suya a Najeriyya ya kasu gida biyu.

(1) yankin da ake kira da GUINEA SAVANNAH- farkon watan yuni (July) zuwa watan yuni (July)

(2) yankin da ake kira SUDAN-SAVANNAH- tsakiyar watan yuni zuwa farkon watan yulin kowacce shekara.


Idan mai-duka ya kai mu mako na gaba zamu dora daga inda muka tsaya inda zamu tattauna akan shin ko waken-suya na bukatar TAKI?
NAGODE

Monday, 14 October 2013

NOMAN WAKEN-SUYA 3

NOMAN WAKEN-SUYA 3  


waken-suya na daya daga cikin manyan amfanin gona na kan gaba da ake sarrafa su a masana'antu da kuma samar da abinci a wannan kasa ta Najeriyya. A kan iya noman waken-suya yayi kyau a cikin  jahohi 36 hade da birnin tarayya  na wannan kasa ba tare da bukatar wani taki mai yawa ko maganin feshin kwari ba. Waken-suya ya samu habbaka a wannan kasa saboda amfaninsa ga tattalin arzikin wannan kasa . Kuma shine kan gaba wajen samr da wadataccen man girki a kasuwannin duniya. Kamar yadda muka fada a baya waken-suya  na kunshe da kashi 40 cikin 100 (40%) na sinadarin furotin (Protein), waken-suya ne kan gaba kan kowace irin cimaka ta dan Najkeriyya irin su sauran amfanin gona ko dabba ko tsuntsaye dake dauke dake dauke da adadin mai yawa na sindarin furotin. Kazalika irin waken- suya na kunshe da kashi 20 cikin 100 (20%) na busashshen mai.

Wani binciken  masana ya tabbatar da cewa bunkasar da aka samu wajen kiwon kaji,talo-talo,kifi da sauransu  a  yan shekarun da suka gabata ya sanya karin bukatar waken-suya a kasuwannin wannan kasa. Binciken kuma ya tabbatar da cewa noman waken-suya ya kara habbaka a wannan kasa saboda yawancin manoman mu sun samu wayewa da kuma amsa kiraye-kiraye da hukumomi keyi domin rungumar noman waken-suya wanda alfanunsa bai tsaya kawai domin ci ko sayarwa ba kawai, a'a saboda muhimmancin sa wajen karawa kasar noma tagomashi ga kasar noma da aka noma shi akai. Dadin dadawa kuma kasuwannin waken-suya na dada habbaka kullu yaumun a wannan kasa tamu, yayin da manoman mu kuma dama ta samu nasamun abin kaiwa bakin salati.

ABUBUWAN LURA KAFIN A SHUKA IRIN WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.

Yanayi mai kyau da kuma kasar noma ingantacciya suna da  tasiri sosai wajen samun amfani mai yado.  Waken-suya yana yin kyau a dukkan yankunan wannan kasa wato yanki kudanci da kuma arewaci, inda yawan adadin ruwan sama yakai alkaluma 700 na ma'aunin (mm). Hakanan lokacin da yafi kamata manoma su shuka wakaen-suya ya ta'allaka da yanayi da kuma wajen da za'a noma waken-suya. Manoman waken-suya a najeriyya na iya noma shi a kowace gona da dandananta ya kai lissafin alkalami 4.5 zuwa 8.5 na ma'aunin (ph). ya kamata manoman waken-suya su lura da cewa ba'a noman waken-suya a gona mai yashi,ko ma tarin duwarwatsu, ko mai kwari ko kuma mai hyawan kwazazzabai.

KIN TSA GONA KAFIN SHUKA WAKEN-SUYA A NAJERIYYA.

(1) SHARAR GONA :



Ana bukatar a kau da dukkanin ciyayi kafin shuka waken-suya. Ramin iri kuwa za'a iya shirya shi ta hanyar amfani da fatanya, ko garmar shirya ko kuma ta yin amfani da motar tarakta (Tractor).  A kula da cewa gonar da aka kintsa ta sosai don shuka waken-suya ko kowanne irin amfanin gona yana tabbatar da saurin yin tsiro da  kuma  rage  tasirin ciyayi   a cikin gona. Hakanan  manomi zai iya shuka irin waken-suya a kan kunya koma ba'a kunya ba.

(2) ZABEN IRIN NOMA:




A kowanne lokaci manomi ya tashi zaben irin noma ba kawai na waken-suya  ba, ya tabbatar ya zabi  irin da ya dace da yanayin yankin  da  yake.  Zabin irin noman waken-suya, wajibi ne ya zama kan saurin yin tsiro, yawan yado, juriya daga fari  ko kamfar ruwa da kuma jajircewa kwari da sauran  cututtuka   masu addabar waken-suya.  Wajibi kuma manomi ya lura da cewa lokacin nunar irin waken-suya shine farkon  abin lura  wajen zaben  irin waken-suya  da ya dace da yankinsa.


Yana da kyau manomi ya zabi irin waken-suya mai saurin nuna kan wanda kan wanda baya  nuna da  wuri a wajen da yake da  karancin  ruwa  ruwa.  Duk da cewa  wadansu manoman suna ganin noman irin waken suya mai dogon   zango (wanda  baya nuna  da  wuri)  yafi yado,  amma fa tabbas ya kamata  manoman mu na waken-suya su fahimci iri hadarin da yake tattare  da noman waken-suya mai dogon  zango  a  yankin da  yake da  kamfar ruwan-sama   saboda  tsoron  fari.


(3) GYARA IRIN WAKEN-SUYA DA SHIRYA SHI A NAJERIYYA:

Shawarar mu ga manoman mu na waken-suya shine a kullum kuyi  amfani da iri mafi inganci  wajen shuka, saboda  irin waken-suya  nan da nan yake rasa  karsashin sa. Wannan kamar  yadda muka sani  gama-garina, domin kuwa waken-suya  koda  ammasa ajiya mai  kyau ba zai yi  tsiro ba  bayan wata 12 zuwa 15 na ajiya.  Saboda haka yana da kyau manoman mu su  zabi Irin waken-suya  da bai kai  wata  12  da ajiya ba.  Yana da kyau  manomi ya zabi Iri masu kyau  daya tabbatar  ba kwaron daya kusance su, ko wata  cuta, ko kuma yana  hade da wani Iri na ciyawa.  Manomi  kada ya sai Iri a cikin  kasuwa  wanda bashi da  tabbas na ingancin Irin, domin kuwa  shuka  Iri mara  kyau ba zai ba da amfani  mai yado ba. A koda yaushe  monomi ya tabbatar ya sai Irin waken-suya a kamfanunuwan da suke sai da Iri ko kuma masu sarrafa  Irin waken-suya da suke kusa da ku.


 Da yardar mai-duka zamu dora in Allah tabaraka wa ta'ala ya kai mu mako na gaba. Kuma ina godiya da sakonnin fatan alkhairi da nake samu daga gareku, da fatan Allah ya saka muku da alkhairinsa.  NAGODE.

Monday, 7 October 2013

    NOMAN WAKEN-SUYA 2

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu mai albarka wanda muke tattauna al'amuran da suka shafi noma da kiwo da kuma yin bincike mai zurfi akan wannan harka ta noma da kiwo da kuma tsokaci kan hanyoyin zamani domin amfanin manoman mu na karkara da masu sha'awar shiga wannan harka don cicciba tattalin arzikin kasarmu da al'ummarmu. Idan masu karatu suna tare damu a wancan makon mun fara tattaunawa ne akan noman waken-suya da yardar mai-duka zamu dora. Allah kadai muke roko da yai mana jagoranci akan dukkanin al'amuranmu.

WAKEN-SUYA : ABINCI


Waken-suya na daya daga cimakar dan-adam masu gina jiki da sanya kuzari, musamman in mukai kyakykyawan duba na tsanaki da kuma kuma nazari kan muhimman sinadaran gina jikin nan da ke kunshe a cikin waken-suya:kamar yadda binciken masana ya nuna kaso 40 cikin 100 (40%) na waken-suya na kunshe da sinadarin furotin (protein), kashi 35 cikin 100 (35%) na kunshe da sinadarin kabohaidiret (carbohydrate), kashi 20 cikin 100 (20%) na kunshe da mai wato (fat oil) yayin da ragowar kashi 5 cikin 100 (5%) na waken-suya ke kunshe da sinadarin Ash (ash). Binciken masanan bai tsaya anan ba inda ya tabbatar da cewar waken-suya na daya daga cikin tsirarun amfanin gona da suke bada cikakken adadin da jiki yake bukata na sinadarin furotin, wannan shine dalilin da yasa ake amfani dashi sau da yawa a maimakon Nama da Madara.


Wannan yasa kamfanunuwan abincin gwangwani irin su MORNINGSTAR FARMS masu yin cincin din nan na humburger da sausage da sauran su ke amfani da waken-suya domin dandano mai armashi da gina jiki. Dalilin haka ne  ya sanya yawancin cimakar mutanen cana (china), Koriya (Korea), Japan (Japan) da kuma kudu-maso-gabashin Ashiya zaka samu akwai waken-suya. Hakanan kamfanunuwan yin madara ma ba'a barsu a baya ba wajen yin amfani da waken-suya domin yin madarar waken-suya da sauransu. Kazalika a wannan yanki namu ma akan sarrafa waken-suya domin yin Awara da sauran abinci masu gina jiki. A takaice dai waken-suya akan iya sarrafa shi nau'i daban-daban daya hadar da yin mai, garin fulawa da kuma abinci na dan-adam ko na dabbobi.




WAKEN-SUYA: AMFANI
A wadansu kasashen kamar su Amurka da nahiyar turai sun dogara da man waken-suya domin dafe-dafen abinci. Kazalika waken-suya ma ya samu kyakykyawar kulawar masana  kamar sauran amfanin gonakin damu ka tattauna inda masana kan kimiyyar noma sukai dogon bincike tare da fitar da wani nau'i na waken-suya wanda suka sauya halittar sa da ake kira da GENETICALLY-MODIFIED SOY wanda a takaice ake kira da (G.M.O).   G.M.O an fitar dashi domin manoman waken-suya, yana da juriya daga kwari gashi baya bukatar wani taki ko noma mai yawa. Wannan dalilin yasa manoman waken-suya sukai amanna dashi inda kashi 8 cikin 100 (8%) na manoman waken-suya ke amfani dashi a shekarar 1997 zuwa kashi 92 cikin 100 (92%)  a halin yanzu (2012).

Kazalika waken-suya yana taka muhimmiyar rawa game da kariya ga lafiyar dan-adam, musamman kasancewarsa magani kafiyan ga matsananciyyar cutar nan ta Daji wato (Cancer) da sauran cututtuka masu kama da haka, wannan binciken yazo ne akan maganganun da ake yadawa kan cewar waken-suya yana kawo cutar daji. Baya ga haka  akan shafa man waken-suya ga fatar jiki domin samun  kariya  daga  cizon sauro,kwarkwata, kudin-cizo da sauran miyagun kwarirrika.





WAKEN-SUYA: NOMANSA


Kamar yadda muka fada kasar  Amurka itace a gaba duk fadin duniya wajen noman waken-suya inda kasar Barazil wato (Brasil) ke mara mata baya yayin da kasar mu Najeriyya ke jagoranci a nahiyar Afirika (Africa) inda kasar Afrika-ta-kudu wato (South-africa) ke mara mata baya , duk da cewa a yan kwanakin nan alkaluman yawan adadin noman waken-suya na yin kasa a can kasar ta Amurka sakamakon karanci filaye da gonakin noma. A shekarar data gabata (2012) kawai an girbe Tan miliyan 224.2 (224.2 million metric ton) na waken-suya inda akwai kyakykyawan tsammanin nan da yan shekaru masu zuwa yawan waken-suya  da ake nomawa a duniya  zai kai Tan miliyan 280 saboda yawan bukatarsa a kasuwannin duniya. Idan muka dawo yankinmu kuma na Afirika kuma zamu ga ana noma abin da ya kai tan miliyan 1.8 na waken suya duk da yawan wannan adadi kasashen Afirika na shigo da abin da yakai tan 20,000 na waken-suya daga kasashen ketare.

Noman waken-suya dan kasuwancinsa a kasuwar duniya, kasashen Zambia,Zimbabwe da kuma Afrika-ta-kudu na kan gaba inda suka ware tafka-tafkan gonaki domin gudanar da wannan harka. Amma akasarin manomanmu na noman waken-suya na noman  don ci a gida, inda suke nomansa yawanci tare da Dawa,Gero,Rogo da sauransu.

Anan zamu dakata sai mai-duka ya kai mu mako na gaba inda zamu tattauna kan noman-waken suya a kasarmu Najeriyya musamman ma a wannan yanki namu na arewacin wannan kasa. NAGODE.

Monday, 30 September 2013

NOMAN WAKEN-SUYA (1)

                                            NOMAN WAKEN SUYA




Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan dandali namu na noma da kiwo inda muke tattaunawa akan  al'amuran da suka shafi noma da kiwo don bunkasa tattalin arzikin al'umarmu,yankinmu da kuma kasarmu baki daya. A wannan makon da yardar mai-duka zamu tattauna akan noman waken suya. Da fatan masu karatu za'a kasance damu.



GABATARWA

Waken suya na daya daga cikin amfanin gona da aka sansu tun da dadewa a can nahiyar ASHIYA (Asia), wanda suke noman sa dan samar da mai,madara da kuma sauran sinadaran kara kuzari irin su PROTEIN da sauran su. Ana noman waken suya ne a waje mai yanayin zafi. Ainihin manoman waken suya kamar yadda binciken masana ya nuna suna noman shine don samar da takin gargajiyya sakamakon yawan sinadarin nan na NITROGEN da yake kunshe dashi. Musamman ga manoma masu yin noman kewaye wato (crop rotation) inda ake shuka shi a matacciyar gona bayan ya  fito sai su bi shi da kasa su binne daga baya kuma sai a shuka amfani.

Cigaban da aka samu na fasahar zamani ta hanyar sarrafa da adana man waken suya yasa aka samar da hanyoyin amfani dashi daban-daban, wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna akan abin da ya shafi tarihi,asali da cigaban da aka samu a duniya wajen noman waken-suya,wannan ya kunshi  nomansa,cututtuka da kwarikan dake addabarsa da yadda za'a magancesu,yadda ake zuba taki da girbinsa da yadda manomi zai adana shi, da kuma uwa-uba yin tsokaci kan irin muhimmiyar gudummawar da waken-suya ke bayarwa wajen cicciba tattalin arzikin duniya.


TAKAITACCEN TARIHI


Kamar yadda muka fada, yankin Ashiya (Asia) shine yanki na farko kamar yadda masana suka fada da aka fara noman waken-suya,wanda suke noman sa a matsayin dangin furannin dajin nan  da ake kira da (Glycine soja) kusan shekaru 5000 da suka gabata. Duk da haka, asali da tarihin noman waken-suya ba zai cika ba tare da ambaton wannan shararren jarumin nan na kasar Sin (China) wato SHENNONG wanda akewa lakabi da ''DIVINE FARMER'', masana tarihi sun tabbatar da cewa oshine wanda ya kawo fasahar noma ga mutanen kasar Sin da kuma Biyatnam (Vietnam), ance ya sanya wken-suya a cikin furannin daya kira ''Tsarkakakkun furanni guda biyar'' wanda suka kunshi shinkafa,alkama,dawa da kuma gero. Hakanan a shekara ta 1000 kafin haihuwar Annabi Isa aka fara noman waken-suya a kasar Jafan (Japan) da Koriya (Korea) wato tun  a zamanin mulkin Rumawa.
Waken-suya yana daga cikin dangin Legum wanda ya hada da wake da sauran su. Wannan dangi shine na uku mafi girma a dangin furannin kallo, dake dauke da dangi kala-kala har kusan 15,000. Waken-suya a kewaye yake yana dauke da launin ruwan dorawa-dorawa. Saboda yawan maikon da yake dashi da kuma sinadarin PROTEIN daya kunsa yasa akan iya sarrafa waken-suya ta hanyoyi daban-daban domin amfani iri-iri.

Masana tarihi sun tabbatar da cewa noman waken-suya ya bulla a nahiyar turai da kasar Amurka tun a lokacin mulkin mallaka. Hakanan manoman yankin Ashiya sun fara noman waken-suya ne ka'in da na'in a shekarar 1910. Tun daga sannan noman waken-suya ya habbaka a wannan yanki, inda a halin yanzu kasar Amurka ke jagoranta da kashi 55 cikin dari wato (55%) yayin da idan muka dawo yankin mu na Afirika kuma kasarmu ce ta Najeriyya ke jagoranta yayin da kasar Afirika ta kudu (South-africa) ke rufa mata baya.

Da yardar mai-duka zamu dora a mako na gaba. NAGODE

Monday, 23 September 2013

                                                    NOMAN AUDUGA 2


NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA

Masu karatu da fatan kuna tare da mu kuma kun ji dadin mukalar mu ta makon da ya gabata , a yau da yardar mai duka muna dauke da karashen wannan mukala da muke tattaunawa akan noman auduga.


Noman auduga a Najeriyya musamman ma a wannan yankin namu yafi karkata da yin amfani da katti yayin da a sauran sassan duniya ake amfani da taraktocin noma da injina da saukaka wa da kuma saman amfani mai yawa. Auduga na tsananin bukatar ruwa tare da magungunan kashe kwari (wanda binciken masana ya tabbatar da akwai jinsinan kwari sama da 1300, ciki wanda 500 suna wannan nahiyar tamu ta Afirika da suka dogara da auduga dan samun abinci) da kuma wadataccen taki. Bisa ga haka ne ma kasashen Amurka da Hindu wato (India) suka samar da wanisabon irin auduga wanda suka sauya fasalinsa ta hanyar binciken kimiyya wanda suke kira da (Genetics) ko (Genetically modified cotton) ko (GM) a takaice. GM cotton na da tsananin juriya daga kwari da rashin ruwa da kuma sauran cututtuka. Dadin dadawa kuma kwari basa iya cin sa saboda dafin dake tare da shi.
Auduga na bukatar lokacin noma mai tsayi, kasa mai yawa, da haske ga kuma uwa-uba ruwa wanda ake bukatar akalla zira'i biyu, binciken masana harkar noma suntabbatar da saboda bukatar ruwa da auduga ke bukata ya zama silar kwararowar hamada a yankunan tsohuwar tarayyar sobiyat wato (U.S.S.R). A halin yanzu kasar Amurka da sauran kasashen nahiyar Afirika ke jagorantar noman auduga a fadin duniya.


Najeriyya ma ba'a barta a baya ba wajen noman auduga, a matsayinta na daya daga cikin ginshikan ci gaban tattalin arzikin wannan kasa da kuma samar da kudaden shiga tun daga hshekarar 1903 zuwa yau. A kokarin gwamnati na ganin ta bunkasa wannan harka ta noman auduga yasa ta kafa hukumomi da kwamitoci daban-daban don bada shawara kan yadda za'a bunkasa wannan harka. Wadannan hukumomi da kwamitoci siun  hada da British Cotton Growers Association, har ya zuwa shekarar 1974 inda aka maye gurbin ta da Cotton Marketing Board. A sabili da tsarurrukan gwamnati na sauya fasalin tattalin arzikin wannan kasa yasa gwamnati ta rushe wannan hukuma tare da dakatar da ayyukanta tare da kafa wani kwamitin tuntuba a madadinta wanda ta kira da Cotton Consultative Commitee (CCC). Wannan bai tsaya anan ba a shekara 2005 an sake kafa  wani kwamiti mai suna Cotton Development Commitee wanda aka dora alhakin farfado da noman auduga ta hanyar amfani da fasahar zamani don cigaban kasa.


NAHIYOYIN NOMAN AUDUGA A NAJERIYYA
Duk shekara a noma auduga a abin da ya aki kadada sama da miliyan 0.2-0.6 inda tsaunukan Savannah ke jagorantar kaso mafi yawa. A shekarar 2007-2008 kawai an noma akalla tan 400,000 na irin  auduga a kadada miliyan 0.3. Noman auduga a Najeriyya ya kasu izuwa manyan shiyoyi guda uku sune: shiyyar arewa ke da kashi sittin cikin dari (60%), shiyyar gabas nada kashi talatin cikin dari (30%), yayin da shiyyar kudu keda ragowar kashi goma cikin dari (10%). Kananan manoma masu gona mai girman kadada 3-5 ne suka mamaye noman auduga a najeriyya.




KAMMALAWA 
A karshen wannan mukala ba zamu gajiya kan kira ga mutane da gwamnati kan wajibcin mu na koma da rungumar harkar noma ka'in da na'in domin cicciba tattalin arzikin kasarmu. Gwamnati na da kyakykyarawar da zata taka wajen bunkasa noman auduga ta hanyar tallafawa manoman auduga da kuma karfafawa masu zuba jari kan masana'antun samar da tufa a Najeriyya wadda ita ce masa'anta ta uku wajen tallafawa tattalion arzikin wannan kasa in ka cire danyan man fetur (crude oil) da noma sai masana'antun tufafi wato (textile industries) wanda suka dogara kacokan kan auduga dan yin ayyukan su. Sai mun hadu a mako na gaba. NAGODE

Monday, 16 September 2013

NOMAN AUDUGA 1

                                                  NOMAN   AUDUGA

 Masu karatu inai muku sallama tare da fatan alkhairi da kuma jinjina dan gane da jumurin karatu da kuma fatan alherin da kuke mana tare da kuma neman afuwar ku dangane da shirun da aka ji na yan kwanaki, wannan kuwa ya faru ne saboda tutsun na'ura da muka fuskanta, da fatan za'ai mana afuwa kuma a cigaba da kasancewa damu.A yau zamu tattauna kan abin da ya shafi noma da kasuwancin auduga a kasarnan.

Auduga na daya daga cikin kayan amfani gona da ake sarrafa su dan amfani iri daban-daban, wanda ya hada da sarrafa auduga don samar da tufafin sawa,samar da takardu,samar da magani,samar da mai da sauran kayan abinci. Auduga ana noman ta a ko'ina cikin fadin duniyar nan tamu, yayin da musayar kasuwancinta a kasuwar duniya ya kai sama da Dala biliyan 12 a duk shekara inda kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirika ke jagoranta da kaso mafi rinjaye. Wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna takaitaccen tarihin auduga,ire-iren ta,kasuwancinta,noman ta a yau da kuma bayanin yadda ake sarrafata don amfanin mu na yau da kullum.

TAKAITACCEN TARIHI
Auduga ko Al-qutn da yaren Larabci (Arabic), na daya ga cikin dangin furannin fulawoyin kallo wato (flowering plant). Akwai sanannun ire-iren auduga guda hudu. Akwai wadda ake kira da GOSSYPIUM HIPSUTUM wadda aka fi noman ta a kasashen Amurka,Mexico da kasashen karebiyan (carrebian).Sauran sun hada da TREE-COTTON wadda aka fi noman ta a kasashen Hindu (India) da Pakistan, sai BARBADEBSE ta kasashen kudancin Amurka da kuma LEVANTINE wadda ake noman ta a kasashen Afirika da kuma kasashen gabas ta tsakiya wato (Middle -east).

Masana tarihi sun tabbatar da an fara noman auduga kusan shekaru 6000 da suka gabata, a daular Harrafawa (Harapan) da ke yankin Asiya (Asia), daga nan noman auduga ya bazu,ya yadu zuwa fadin duniya inda Manoma suka dukufa ka'in da na'in wajen nomanta gwargwadon irin yanayin da Ubangiji ya hore musu.

AMFANIN AUDUGA
Auduga na da matukar amfani ga dan-adam ta yadda masana suka tabbatar da cewa matukar mutane zasu rayu to tilas suyi noman auduga. Domin kuwa baya ga amfani da auduga da ake yi don saka sutturun sawa, hakanan ana amfani da ita danyin zaren lilo,ragar kamun kifi,likkafani da sauransu. Saboda yawan alfanu da juriya da biyan bukata na auduga yasa masana'antun tufafi suka dogara kacokan kan auduga don biyan bukatun su.

Kazalika ana amfani da auduga dan magani,abinci da kuma samar da takardu. Kwallon auduga ana amfani dashi wajen dafa abinci sannan kuma naman ta akan ba dabbobi su ci.

Idan maiduka ya kai mu mako na gaba zamu dora. NAGODE.